’Yan Nijeriya Da Ke Da Kadarori A Ingila Sun Shiga Fargaba Sakamakon Sabbin Dokoki

‘Yan Nijeriyan da suka mallaki filaye da gidaje a Kasar Ingila, sun addabi sashen bayyana kadarori na Ma’aikatar kudi ta Tarayya da kiraye-kiraye a ranar Juma’a, wanda hakan har ya kai ga rugujewar layin wayar sashen na ma’aikatar kudin.

Wata majiya daga Ofishin ma’aikatar ta kudi, ta shaida mana cewa, kiraye-kirayen da masu kumbar susan suka addabi ma’aikatar ta kudi da su, ba sa rasa nasaba da sabuwar dokar da gwamnatin Ingila ta fitar, a kan kadarorin da ba su da cikakkun bayanai da ke cikin kasar.

Majiyar ta tabbatar mana da cewa, Ofishin na su,sun yi ta samun kira ba kakkautawa ne daga ‘yan kasan nan mazauna Ingila, suna neman da a tsawaita masu lokacin da za su kammala cike takardun su na bayanin kadarorin na su.

A satin da ya gabata ne dai, Kasar ta Ingila ta fitar da wata sabuwar doka, wacce ta bukaci dukkanin bakin da ke zaune a cikin kasar da kuma wadanda suke da mallakan duk wata kadara a cikin kasar ta Ingila, da su yi mata bayani filla-filla na yadda aka yi suka mallaki wannan kadara, idan kuwa sun gaza yin hakan, kasar ta Ingila za ta iya mallake wadannan kadarorin.

Kamar yadda sabuwar dokar ta nu na, tilas ne a samar da bayani a kan duk wata kadara da mutum ya mallaka shi kadai ko ta hanyar hada hannu wacce kimarta ya kai Fam 50,000, watau kimanin Naira Milyan 25 kenan,ko fiye da hakan. Duk wanda ya mallaki hakan kuma ya kasa ya yi bayanin halastacciyar hanyar da ya bi wajen mallakanta, shikenan kadarar ta zama ta gwamnati.

Bayanan da suka fito daga  Ma’aikatar sun nu na cewa, mafiya yawan masu mallakan kadarorin a kasar ta Ingila, ba su biya wa kudaden su haraji ba kafin su maida su kasar ta Ingila domin sayen gidaje da filaye.

Ma’aikatar dai tana ta aiki tukuru domin gyara layin wayar na ta da ya lalace a sakamakon yawan kiraye-kirayen a ranar ta Juma’a.

“Yawancin masu kiran dai, duk manyan mutane ne, da suka hada da shugabannin kamfanoni, manyan ma’aikatan Bankuna kai har ma da wani Gwamna. Duk cikinsu ya duri ruwa, domin sun tabbatar da suna gab da rasa kadarorin na su.

Bayanan nan ma sun nu na,lamarin ya kai ga hatta wasu da suke jin su isassu ne, sun yi takakka har zuwa ma’aikatar suna bukatar ganin Minista ido-da-ido, da kuma shugaban sashen binciken kadarorin, domin neman hanyar da kadarorin na su za su kubuta.

Da yawa dai daga cikin manyan kusoshin da suke ta wadarin kiraye-kiraye da kuma takakka zuwa Ofishin ma’aikatar, bukatar su shine, su sami tabbacin gwamnatin Tarayya za ta kare masu kadarorin na su, domin ka da su rasa su ga gwamnatin ta kasar Ingila. Wasu kuwa hankoronsu shine su tabbatar ko sunayen su suna cikin jerin sunayen da gwamnatin ta kasar Ingilan ta fitar ko a’a.

Exit mobile version