Connect with us

KIWON LAFIYA

‘Yan Nijeriya Na Zukar Karar Sigari Biliyan 20 A Duk Shekara

Published

on

Fiye da karan sigari Biliyan 20 ake zuka a duk shekara a Nijeriya, a cewar Ministan lafiya Mista Isaac Adewole.
Mista Adewole ya kuma ce, magidanta fiye da Miliyan 4.5 suna amfani da abubuwan da suka shafi sigari yayin da mutane kashi 85 dake ziyartar gidajen giya da sanran wuraren masha’a ke zama masu shan sigari a mataki na biyu.
Ministan ya yi wadannan bayanin ne a yayin taron manema labarai domin bukin ranar shan sigari ta duniya (2018 World No-Tobacco day) wannda ya gudanar ranar Litinin a Abuja, ya kara da cewar, a shekarar 2015 an kiyasta cewar, kasar na tayi asarar Dala Biliyan 7.6 a kan abubuwan da suka shafi taba sigari.
Ana bukin ranar kawar da sigari ta duniya “World No Tobacco Day” ne a duk ranar 31 ga watan Mayu na duk shekara, taken bukun na wannan shekarar shi ne dangantakar sigari da shan sigari, “Tobacco and Heart Disease.”
“Bari in janyo hankalin jama’a a kan cewa, amfani da taba sigari ya yi sanadiyar gaggarumar asarar kudade a kana bin daya shafi magunguna da kiwon lafiya” inji Mista Adewole.
“An kiyasta cewa, Nijeriya na asarar fiye da Dala Miliyan 800 a sanadiyar cututtukan da suka hada dana shanyewar jiki da cututtukan zuciya da kuma ciwon suga.
“A shekarar 2015 an kiyasta asarar da aka yi a sanadiyar zukan taba sigari ya kai Dala Biliyan 7.6” inji shi.
Ya kuma kara da cewa, a cikin duk ribar dala 1 da ake samu a harkar taba sigari ana kashe Dala 3 wajen dawainiyar maganin cututtukan da suka danganci shan taba sigari, ya kuma lura cewa, kanfanonin taba sigari da samun dimbin riba basa kuma daukar dauyin barnar da suke yi a fannin lafiyar al’umma.
Daya ke bayani a kan taban nan da ake kira shisha, Mista Adewole, ya ce, Nijeriya ba zata amince da zukan sigari ta kowanne hanya ba saboda a kwai hakkin kare rayuwar alummar kasar nan daga fadawa cuta.
“Sakamako mai mahimmanci shi ne haramta sanya wasu kanshi minti a cikin taba domin yaudarar mutane su shiga sha taban”
“A yanke wannan shawarar don kare ‘yan rayanmu daga yaudarar kashin minti. Bari in kara nanata cewa, an haramta duk wani abin daya shafi taba sigarin dake dauke da kanshin minti sa sauransu, an kuma haramta sigarin da ake sha mai suna shisha saboda shi ma yana da kanshin minti”
“A saboda haka ina kara kira ga hukumar kare masu amfani da kayyaki “Consumer Protection Council (CPC)” da sauran hukumomin tsaro dasu zafafa kama masu karya wadannan dokokin” inji shi.
A nasa jawabin a wajen taron, wakilin hukumar “World Health Organisation (WHO)” a Nijeriya, Wondi Alemu, ya ce, dakile yaduwar shan taba sigari shi ne hanya mafi sauki na cimma daya daga cikin muradun karni na “Sustainable Debelopment Goals (SDGs)”, wanda ya keda burin karewa da kawar da mutuwar daga cututtukar da suka shafi wadanda ake dauka tsakanin jama’a nan da shekarar 2030.
Ya ce, kawar da amfani da taba sigari zai taimaka wajen lare miliyoyin mutane daga mutuwa sakamakon cututtakar da ba za a iya dauka tsakanin mutane ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: