ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Sama Jannatin Sin Na Gudanar Da Muhimman Atisaye Da Gwaje-Gwaje A Tashar Sararin Samaniya

by Sulaiman
8 months ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-21 da ke tashar sararin samaniya ta Tiangong ta kasar Sin sun kammala jerin atisayen samun horo mai mahimmanci da gwaje-gwajen kimiyya masu zurfi a cikin sararin samaniya, inda suka kafa harsashi mai karfi na ayyukan da za a gudanar nan gaba da kuma binciken kimiyya.

Wani rahoto na bidiyo da rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya nuna a jiya Lahadi da dare, ya nuna ‘yan sama jannatin suna gudanar da cikakken atisayen gwaji, ciki har da na aiki da na’ura daga nesa a kayyadadden lokaci, da sada ayyukan kumbuna biyu, da hanyoyin gudanar da ayyukan ceto na kiwon lafiya da kuma samun horon kwashe mutane cikin gaggawa, duk a makon da ya gabata.

Kamar yadda aka bayyana a rahoton, an tsara wadannan ayyukan ne don inganta kwarewar aikin ‘yan sama jannatin da kuma kai daukin gaggawa a yayin da suke zama na dogon lokaci a cikin kumbon,

ADVERTISEMENT

A cewar rahoton, domin samun horon iya aiki da na’ura daga nesa a lokacin sada ayyukan kumbuna biyu, ‘yan sama jannatin sun yi amfani da hannu wajen sarrafa na’urori don kwaikwayon yadda ake tafiyar da tsarin jagorancin kumbuna a sama. Atisayen bangaren kiwon lafiya kuwa, ya fi mayar da hankali ne kan fahimtar da ‘yan sama jannatin game da wuri da yadda ake aiki da kayan kiwon lafiyar, tare da yin bita kan ka’idoji domin tabbatar da an kimtsa tsaf wajen shawo kan matsalolin kiwon lafiya idan sun taso. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Sin
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
  • Sulaiman
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • Sulaiman
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

MASU ALAKA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
Daga Birnin Sin

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Next Post
Ƴansanda Sun Kama Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Da Wasu Mutane Biyar A Kano

Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.