‘Yan Sanda Sun Kama Bokan Da Ya Binne Samari Biyu Da Ransu A Ebonyi – ‘Yan Sanda

Daga Mahdi M. Muhammad,

Rundunar ‘yan sanda a Ebonyi ta bayyana dalilin da ya sa aka binne wasu samari biyu da ransu a cikin wani kabari mara zurfi a cikin dajin Uduku-Igbudu a Agubia, karamar hukumar Ikwo da ke jihar.

NAN ta ruwaito cewa a ranar 30 ga watan Afrilu ne ‘yan sanda suka gano ragowar jikin samarin biyu da aka ce wadanda suka sace su sun binne su da ransu a cikin dajin.

‘Yan sanda sun kuma kama wasu likitoci gargajiyar biyu wadanda suka kasance ‘yan asalin Ebonyi ne a kan laifin.

DSP Lobeth Odah, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na Ebonyi ta shaida wa NAN cewa, an rufe idanuwan mamatan yayin da aka daure igiyoyi a wuyansu lokacin da ‘yan sanda suka zakulo gawarwakinsu da suka rube.

“Mun je daji tare da kwararru kuma an fitar da gawarwakin an mika su ga danginsu don binne su, da kuma binciken ‘yan sanda na matakin karshe,” in ji ta.

A cewar PPRO ya yi bayanin cewa likitocin ‘yan asalin biyu da aka kama ana zargin sun sace samarin biyu a ranar 12 ga Afrilu don matsawa danginsu su janye karar da ta shafi yaransu a kotu.

“Ee, ‘yan kasa suna da ikon shiga kowane addini amma idan ya shafi saba doka, ba za a yarda da hakan ba. Ku guji haramtattun kasuwanci ta amfani da addini, ‘yan sanda za su kame duk wanda ke yin hakan, koda kuwa mutumin likitan gargajiya,” in ji Odah.

Kakakin ‘yan sandan ta kuma gargadi likitocin gargajiya na Ebonyi game da ba masu laifi laya don aikata ayyukan ta’addanci a jihar.

Odah, wacce ta ce rundunar ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyi, don haka ta bukaci likitocin gargajiyar garin na Ebonyi da ma kasa baki daya da su daina kasuwanci ba bisa ka’ida ba.

Exit mobile version