Daga Sagir Abubakar Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta gabatar da wasu mutane 34 da ake zargi da yin awon gaba da kayayyaki na dubban Nairori a lokacin da gobara ta tashi a babbar kasuwar Katsina.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar sufuri Tanda Gambo Isa ya gabatar da wadanda ake zargin tare da sauran wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka.
An kwace kayayyaki daban-daban daga hannun wadanda ake zargin wadanda suka hada da katan-katan na madara, da gari, kayayyakin sawa, janaraitoci, takalma da makamantansu.
SP Gambo ya shaida wa ‘yan jarida cewa, Kwamishinan ‘yan sanda Sanusi Buba ya umarci jami’an rundunar dasu karade dukkanin wata mashigar kasuwar wanda hakan ya taimaka aka damke wadanda ake zargin.
Ya bayyana cewa ana cigaba da bincike domin damke sauran wadanda ake ake zargin don su fukanci hukunci.
Haka kuma, rundunar ‘yan sandn jihar Katsina ta gabatar da wasu mutan daban-daban da ake zargin ‘yan bindiga ne, da aikata laifukan fyade da kuma garkuwa da mutane wadanda suka amsa cewa suna da hannu dumu-dumu wajen kai hare-hare daban-daban a jihohin Katsina da Zamfara.
Haka kuma, rundunar ta samu nasarar ceto wasu mutane (30) da akai safararsu wandanda mafi yawansu sun fito daga kudancin kasar nan.
Wandanda ake kokarin tsallakawa dasu jamhuriyyaar Niger akan hanayarsu ta zuwa Libiya inda daga bisani za’a tsallaka dasu zuwa Turai.