Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Yobe, CP Garba Ahmed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan wani kisan gilla da ya faru da Sufeto Mohammed Bulama, wanda ke aiki da rundunar ‘yan sanda sintiri shiyya ta 41 a Damaturu, babban birnin jihar.
PUNCH Metro ta ruwaito cewa, a cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim ya fitar da misalin karfe 18:20, Sufeto Mohammed Bulama, mai shekaru 38, ya shiga cikin lamarin. An samu zazzafar muhawara da Abdulmalik Dauda (wanda aka fi sani da Baksha) mai shekaru 39 a unguwar Pompomari a Damaturu kan wani ciniki da ba a warware ba a Unguwar Zango.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Rage Kudin Sufuri Da Kashi 40 Ta Hanyar Amfani Da Motoci Masu Iskar Gas
- Tinubu Ya Samar Da Naira Biliyan 29 Don Gyara Hanyoyin Kasar Nan
Sanarwar ta ci gaba da cewa, rikicin ya barke ne, inda ake zargin Bulama ya daba wa Dauda wuka a kirjinsa, lamarin da ya sa ya samu rauni a kansa a yayin arangamar.
Ba tare da bata lokaci ba an kama Bulama a shealkwatar ‘yan sanda ta ‘C’, inda ya nemi mafaka. Hukumar binciken manyan laifuka ta jihar ta fara gudanar da bincike, kuma a halin yanzu Bulama yana tsare har sai an gurfanar da shi a gaban kotu.
Ahmed ya yi Allah-wadai da abin da Bulama ya aikata, ya kuma jajantawa iyalan Dauda, tare da ba jama’a tabbacin gudanar da cikakken bincike da gaggawa domin tabbatar da adalci.
“Rundunar ‘yansandan Nijeriya ba za ta amince da duk wani rashin da’a daga jami’anta ba. Za mu tabbatar an yi adalci tare da hukunta wanda ya aikata laifin,” in ji Ahmed.