‘Yansanda a jihar Jigawa sun kone maboyar masu garkuwan da suka dade suna addabar wasu sassa a jihar Kano da Jigawa da kuma Katsina.
Nai nagaba da yawun rundunar ‘yansanda na jihar, DSP Lawan Shiisu Adam ne ya tabbatar da faruwar hakan, a wata takarda da ya raba wa manema labarai.
- Tsegunta Barazanar Tsaro Daga Ofishin Jakadancin Amurka: Wa Abin Zai Amfanar?
- EFCC Ta Kai Samame Haramtacciyar Kasuwar ‘Yan Canji Da Ke Abuja
Ya ce, sun babbake maboyar masu garkuwan ne sakamakon wani rahoton sirri da suka samu kan wasu miyagun ayyuka da ake yi a wannan guri.
Kamar yadda bayanin ya nuna, ranar Litinin rundunar ‘yansandan ta samu nasarar kama wani hamshakin mai garkuwa da mutane mai suna Muhammad Bello da ke Dunkura Sullubawa a jihar.
Ya ce, wanda ake zargin ya amsa laifinsa na cewa shi ya hada ‘yanfashin a Shuwarin da Aujara da Yalleman da kuma Dakaiyyawa da ke jihar Jigawa suke yin garkuwa da mutane a jihar Katsina.
Shiisu ya ce, wanda aka Kaman yana bayar da bayanai da za su taimaka wajen gano sauran wadanda suka aikata laifin.
Ya ce, har yanzu suna nan suna ci gaba da bincike, da zarar kuma sun gana za su gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu.
Ya ce, rundunar ‘yansandan ta jihar Jigawa krkashin jagorancin, Emmanuel Ekot na kira da babbar murya ga al’ummar jihar da su sanar da ‘yansanda dukkan wani abu da ke matsayin barazana ga zaman lafiyarsu.