Connect with us

LABARAI

’Yantar Da Majalisun Jihohi Ba Fada Ne Da Gwamnoni Ba – dan Majalisa

Published

on

Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Ahmad G. Ahmad, Wakilin Jangero mai wakiltar karamar Hukumar Shinkafi a majalisar, ya bayyana cewa, bai wa majalisun jihohi yancin cin gashin kai, ba ya nufin fada da gwamnonin jihohin Nijeriya ko’ina.

Hon. G. Ahmad ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da ‘yan jarida a zauren majalisar da ke Gusau, babban birnin jihar.
dan majalisar, wanda wannan shi ne karo na biyu na dawowarsa majalisar, ya kara da cewa, abu uku ne ginshikin gwamnati, wato Majalisar Zartarwa, Majalisar Dokoki, sai kuma bangaren Shari’a, kuma kowane na karfafar juna wajen cigaban al’umma ne. Don haka ba kowacce damar cin gashin kansa zai taimaka gaya wajen yi wa al’umma ayyukan more rayuwa kuma garkuwa ne na daina shigar wa wani bangare aikinsa.
“Ba kamar yadda wasu ke tunanin wai bada gashin kan zai jawo fada da gwamnoni ba ne ba, don ayyukan majalisar zartarwa karkashin jagorancin gwamnoni, danjuma ne da danjummai ne wajen tafiyar da ayyukanmu. Don haka babu matsalar da za a samu,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: