Muhammad Sani Chinade" />

Yau Dalibai Masu Jarrabawar Karshe Ke Fara Komawa Makaranta A Yobe

Gwamnatin Jihar Yobe ta hannun ma’aikatar ilimin jihar ta ba da sanarwar sake bude makarantunta a mabambanta lokuta tun bayan rufe su na tsawon lokaci sakamakon annobar cutar nan ta mashako da ta addabi dukkannin duniya, korona.

Sanarwar da aka bayar na nuna kan cewar daliban makarantun da ke matakin aji uku SS 3 na babbar Sakandaren kwana za su koma ne a ranar jumu’ar nan 8 ga watan na Agustan 2020 yayin da daliban babbar makarantar sakandare GDSS na jeka-ka-dawo da kuma na masu zaman kansu, su kuma za su koma a ranar Litinin 11 ga watan na Agusta.

Don haka ne Ma’akatar ilimin ke shawartar dukkannin daliban da abin ya shafa da su tabbatar da sun tanadi takunkumin rufe baki da hanci (facemask) yayin dawowa, inda su kuma hukumomin makarantun za su tanadi dukkannin abubuwan samar da kariya ga kamuwa da wannan cutar.

Kamar yadda kwamishinan ma’aikatar ilimi a matakin farko da manyan sakandare Dakta Muhammad Sani Idris ya ce, Gwamna Mai Mala Buni ya ba da tabbacin a kullum gwamnatin Jihar Yobe na kokarin bin duk wata dokar da gwamnatin tarayya za ta shimfida dangane bude makarantun.

Dakta Sani Idrisa, don haka ya kira yi daliban makarantun sakandare ‘yan aji uku SS 3, da su shirya don kokarin rubuta jarrabawarsu ta fita (WAEC) wadda za su fara daga ranar 17 ga wannan wata na Agustan 2020 don su samu sakamako mai kyau domin jihar ta yi fahari da su.

 

 

Exit mobile version