Yaushe Nijeriya Za Ta Girma?

Tare da Abdurrahman Aliyu 08036954354

“Najeriya kasa ce wadda ke da yawan al’ummomi, da kuma yalwar arziki a dukkan shiyyoyin kasar. Sannan kasa ce da ke da kwararrun mutane Kama daga kowane irin fanni. A bangaren addini kuma kasa ce wadda al’ummar ta ke da riko da bin addini tun daga Musulman ta har Kiristoci da sauran addinan gargajiya”.

Babban abun tambaya a nan shi ne, har yanzu kuwa Nijeriya ta samu ‘yanci? Ko kuwa dai wasu tsirarun mutane ne suka samu ‘yancin ba wai duka kasar ba? Na sha yiwa kaina irin wannan tambayar amma in gaza samun gamsashiyar amsa, domin duk wanda yasan kasa irin Nijeriya ya san cewa tana cikin abubuwa biyu ne wato Cin hanci da rashawa da mulkin mallaka a fakaice daga jami’an tsaron kasar da wasu mahukunta. Bari mu bi su daya bayan daya mu gani.

  1. Cin hanci da Rashawa shi ne, kusan abin da ya tarwatsa ci gaban wannan kasar da kuma dakushe basirarta da hazakar matasanta, duk wasu hanyoyi da ake bi a tarbiyantar da yara a wannan kasa cin hanci da rashawa sun ma fannonin kakagida. Misali a makarantu musamman na kudi, duk rashin kokarin yaro ba zaka taba ganin ya samu nakasun jarabawa ba, domin ba a son babansa ya cire shi daga makarantar a bar samun abin da ake samu a bangaren shi. Wani babban abun takaici da ke kara durkusar da kasar nan shi ne sai anzo yin jarabawa kamala sakandire in da za a zauna a kwafar ma Dalibai duk jarabawar kuma a basu sui rubuta, duk dakikancin dalibi, alhali a gefe guda ga wasu cen su su na yi da kansu amma malamansu na zaginsu. Haka yaro zai gama kuma a biya mashi jarabawar share fagen shiga jami’a, a wasu wurare da ake kira Special da Turanci, ta yadda yaro ko bai je ba sai ya samu adadin makin da ake bukata, kuma ya isa jami’a nan ma ya ci karo da wasu gurbatattun malaman wadanda zai rika ba kudi yan cin jarabawa kamar yadda aka tarbiyantar da shi, kuma wata rana irin wannan yaron ne zai zama shugaba, shin wanda ka dora bi sa wannan hanyar wace irin barna ka ke tunanin zai yi? Domin komi shi a banza ya ke ganin yazo masa, kuma an tarbiyantar da shi akan kudi zasu iya yin komi ta kowace irn hanya, mai kyau ko marasa kyau.

Me ya sa wannan kasar ba zata yi koyi da a kalla koda kasar Ghana ba, irin yadda ta inganta ilimin kasar ya zama abun kwatance, wanda har mu daga nan Nijeriya muna zuwa cen domin neman ilimi, babban abun day a taimakawa kasar Ghana zuwa wannan mataki hard a yunkurin dakushe satar jarabawa da kuma sake fasalin ilimi yadda zai dace da zamani da kuma al’ummar ko wane yanki, an ya wannan tsarin bai dayan na ilimi da ake gudanarwa a kasar nan zai bule kuwa?

In muka koma sauran bangarori na gina kasa nan ma zaka sha mamaki yadda zaka ga cin hanci da rashawa ne dai ke jagorantarsu. Misali fannin Lafiya a kasar nan yau in dai ba zaka bada cin hanci da rasahwa ba to sai dai kai ta hakuri da rashin lafiyarka, amma kana iya mutuwa ma daga tsaye baka sani.

Na taba kai yaro a asibiti amma abin da ya ban mamaki yadda shi mai kiran sunayen ya ware ni y ace “Oga ka yi alheri kawai yanzu zan kira sunan ka” nai tsaye sai mamakin wannan abu nake ashe haka suke tafiyar da al’amuransu kaji wasu sai zagi suke tun dazu suke amma ga wani daga zuwa an kira shi. Haka kuma na taba zuwa diba wani marar lafiya a asibiti, lokacin da likitan da ke zagayawa domin bayar da magani  yazo ya ga an yi wa wannan marasa lafiya aiki sai, ya kada baki y ace “amma wani abu kuka bada ko? Domin wadancen da ke kwance naga duk sun riga shi zuwa?” sai da ya tafi sai nake tambayar mai jinyar me yasa likitana nan ya yi wannan tambayar? Sai ya ce man ai yasan wani abu suka ba da, domin da ba su bada wani abu ba sai an dauki lokaci ba ayi aikin ba.

Asibiti fa ke nan, in da ake sa ran a tausayawa talakawa, amma ya kasance sai ka ba da cin hanci da rashwa sannan buikatarka ta biya a asibiti.

A bangaren kwangiloli kuwa abun ya yi muni domin da zaran ka bar da dan abun ihisani ga injiniyoyin da ke duba kwangilar to su babu ruwansu duk abinda kaga dama ma kayi, ko da kuwa abinda aka sa ayin zai amfani al’ummar yankin injiniyan ne. haka cin hanji ya dabaibaye duk wasu lamurra na rayuwarmu ta ko’ina ya zama ma mun sauyawa kalamar suna zuwa alheri.

Wani nau’in cin hanci mai ban takaici shi ne wanda ake amsa a basa hanyoyin kasar nan yadda jami’in tsaro zai tare ka ko wane mugun abu ka dauko in dai ka bashi dari ko hamsin yana washe baki zai daga ma hannu ya na kiran a sauka lafiya, ba ruwansa da abun da ka dauko shi dai ai kasallame shi kawai.

Idan za a tsaya a rika bayanin yanayin yadda cin hanji ya yi kakagida alamurran kasar nan to sai akwashe lokaci mai tsawo ana yi, kuma kullum fada ake amma ba lamar gyarawa sai dai kara ta’azzara da abun ke yi.

A kwai kasashe da yawa da suka samu kansu cikin irin wannan yanayin amma suka gyara suka fita daga cikinsa, misali Chana sun yi fama da irin wannan kwamacalar amma da suka dauki matakin gyara yanzu sun zauna lafiya. Duk wani wanda aka samu da cin hanci a hukunta shi, amma a kasar nan ko karamin yaro yasan ba a hukunta masu cin hanci da rashawa, shi yasa kullum abun k eta kara ta’azzara, amma muna fatan wannan gwamnatin ta kara matsa kaimi wajen kowo dokokin da za su yi tasiri ga masu cin hanci da rashawa manya da kanana, domin daga kananan ne ake samun manyan.

  1. Mu’amulla Tsakanin ‘yan Kasa da ‘Yansanda: A wannan kasar ‘yansanda kullum cikin yaudarar mutane suke da yin wani kamfe mai taken “Beli kyauta ne” Amma zaka sha mamaki idan kaje belin din wani a hannunsu yadda za su rika yawo da kai tamkar ka aikata wani laifi na mugun abu. Najeriya duk ‘yancin da ake cewa dan kasa na da shi, to da zarar ya fada yaje neman beli hannun ‘yansandan kasar nan zai shiga wani hali na yawo da hankali in dai bai bayar da wani abu ba mafi sauki shi ne kabada wani abu sub aka wanda kaje belin din kuyi gaba. Abin tambaya a nan kasashen da aka cigaba haka ake dama, beli said a kudi ba kyauta ba? Akwai kasashen da ko kusa basu kai Nijeriya komi ba amma abun takaici ba zaka ji suna kamfen beli kyauta ba, domin kowa ya san ‘yancinsa in ka je beli ba zaka bayar da ko sisi ba. Kuma akwai kyawawar alaka tsakanin ‘yansandan kasar da mutanen gari ta yadda zai yi wuya ma in ba dan sanda nab akin aiki ba ka gane shi dansanda ne.

Amma a Nijeriya ko gidan mai a ka je shan mai ko layin banki zaka ga in dai mutum na da kayan sarki ya wo gaba shi ala dole aba shi duk da cewa ga tarin mutane sun riga shi, haka ma mu’amullar mafi yawan ‘yansandan kasar nan nuna son kai ne da kuma nuna cewa su hukuma ne sun fi karfin kowa. Shawara a nan ya kamata hukumar ‘yansandar kasar nan ta rika shiryawa jami’Anta wasu tarukan bita wadanda za su rika kusantar da su ga jama’a. Domin kasashen da suka cigaba duk haka ake yi, kuma muna ganin irin ribar da suke samu. Kai akwai kasashen da zaka ga har jami’an ‘yansanda ke akwai na musamman wadanda zasu rika ba mutane shawara kan yadda ya kamata su tafiyar da rayuwarsu.

Don haka har yau har Gobe wasu tsiraru ne kawai suka samu ‘yanci a Nijeriya sannan kuma mulkin kama karya ya na nan, tallaka bai isa ya fadi gaskiya ga mahuknta ba, domin shi ba kowa ba ne kuma bai da ‘yanci. Hausawa dai na cewa, “inda akuyar gaba ta sha ruwa nan ta baya za ta sha” kuma in kaji makaho uya ce ayi was an jifa to ya taka dutse. Lallai ya kamata ‘Yan Najeriya su cigaba da gwagwarmayar neman ‘yanci domin har yanzu bai samu ba…

 

Exit mobile version