ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za A Binciki Ɗan Majalisa Kan Rushe Gini Da Cin Zarafin Wani Mutum A Kano

by Abubakar Sulaiman
2 days ago

Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta ba ƴansanda umarnin gudanar da cikakken bincike a kan ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Gwarzo/Kabo, Hon. Muazu Abdullahi-Gwarzo (wanda aka fi sani da Baban Gandu), bisa zargin haɗin baki wajen aikata laifi, da barazana ga rayuwa, cin zarafi, da kuma rushe gini ba bisa ƙa’ida ba.

Wannan umarni ya fito ne ta cikin wata wasiƙa mai kwanan watan 19 ga watan Oktoba, 2026, daga magatakardan kotun zuwa ga Mataimakin Sufeto Janar na Ƴansanda (AIG) mai kula da sashin binciken sirri na shiyya, biyo bayan umarnin Babban Kotun Majistare Mai Lamba 5 da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano.

Taƙaddamar ta samo asali ne daga ƙorafin da wani mazaunin unguwar Danbare a Ƙaramar Hukumar Kumbotso mai suna Sulaiman Isah ya shigar ta hannun lauyoyinsa na kamfanin A.S. Tunkuyau & Associates, kan wani fili da kangon da ya saya wanda a baya ya kasance mallakin ɗan majalisar ta hanyar wasu dillalai. Isah ya yi zargin cewa bayan ya kammala biyan kuɗi tare da karɓar dukkan takardun mallaka, ɗan majalisar ya nuna rashin jin daɗinsa tare da ƙaryata cewa ya sayar da filin, lamarin da ya haifar da sa-in-sa tsakaninsu.

ADVERTISEMENT

A cewar takardar ƙorafin, lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar 16 ga watan Oktoba, 2026, inda Isah ya dawo gida ya tarar da wasu mutane a gaban ɗan majalisar suna rushe gininsa. Da ya nuna musu takardun mallakar filin tare da ciro wayarsa domin ɗaukar bidiyon yadda ake rushe ginin a matsayin shaida, an zargi ɗan majalisar da bayar da umarni cewa: “Ku ƙwace wayar, ku daka min shi,” inda wasu mutane huɗu suka auka masa da duka tare da ji masa raunuka a sassan jikinsa har sai da maƙwabta suka kawo masa ɗauki.

Lauyoyin mai ƙara sun buƙaci rundunar ƴansanda da ta gudanar da sahihin bincike ba tare da nuna son kai ba, suna masu jaddada cewa matsayin Gwarzo na ɗan majalisar tarayya mai ci ba zai ba shi kariya daga fuskantar doka ba idan har an same shi da laifi.

LABARAI MASU NASABA

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

Jaridar Daily Nigeria ta yi ƙoƙarin jin ta bakin ɗan majalisar amma hakan bai samu nasara ba sakamakon rashin ɗaga kiran waya ko amsa saƙonnin tes da aka tura masa, yayin da lauyoyin suka buƙaci a ba mai ƙara da shaidunsa kariya daga duk wata barazana.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
  • Abubakar Sulaiman
    Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

MASU ALAKA

ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai
Manyan Labarai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume
Manyan Labarai

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu
Manyan Labarai

Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

October 24, 2026
Next Post
Karamin Dandalin Tattauna Hada-hadar Kudi Da Aka Bude A Kenya Ya Karkata Ga Batun Zuba Jari A Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya

Karamin Dandalin Tattauna Hada-hadar Kudi Da Aka Bude A Kenya Ya Karkata Ga Batun Zuba Jari A Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya

LABARAI MASU NASABA

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

October 24, 2026
Ya Kamata A Baiwa Muryoyin Kasashe Masu Tasowa Damar Sauraro

Ya Kamata A Baiwa Muryoyin Kasashe Masu Tasowa Damar Sauraro

October 24, 2026
Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

October 24, 2026
Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

October 24, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.