Jam’iyyar hadaka ADC ta nuna damuwa game da yadda zaben cike gurbi ya gudana a ranar Asabar a jihohi 13, a daukacin mazabu 16 na tarayya da ke kasar nan, tana mai cewa zaben ya sake bayyana yadda tsarin zaben Nijeriya ya lalace karkashin shugabancin Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi ta hannun sakataren yada labarrai na jam’iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi, jam’iyyar adawa ta yi nuni da cewa zaben na cike da tashin hankali, sayen kuri’u, magudi da sauran matsaloli na rashin inganci.
- Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama
- Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12
ADC ta kara da cewa ba a wai wa jam’iyyar damar fitar da ‘yan takara ba a duka kujerun da aka fafata a zaben. Saboda haka, ADC take Kallon zaben a matsayin wani matakin da ake ware ‘yan adawa, wanda wannan ya nuna yadda tsarin zaben Nijeriya ya shiga rudani a karkashin mulkin APC.
Sanarwar ta ce, “Abin da ‘yan Nijeriya suka shaida a zaben cike girbi a jiya yana ba da wani tunatarwa kan cewa a karkashin wannan gwamnatin, dimokuradiyya kanta an mayar da ita kamar yadda tattalin arziki da tsaron kasa ke ci gaba da tabarbarewa a karkashin Shugaban Bola Ahmed Tinubu da APC.
“A duk Lokacin da zabe ya kasance cike da tashin hankali da musanya kuri’u da kudi a fili da ware ‘yan takarar adawa ba tare da bayani ba da kuma lokacin da manyan cibiyoyin da ke kare dimokuradiyya suka lalace, to kuri’ar talakan Nijeriya ba ta da wani amfani.
“A wasu jihohi, kusan ‘yan daba 300 aka damke da wukake da adduna a ranar zaben. Shin wannan shi ne dimokuradiyya ko kuma ta’addancin da aka sanya wa suna.
A wasu jihohi, an soke dukkanin zaben saboda satar akwatunan zabe da cin zarafin masu kada kuri’a. Idan ‘yan kasa ba za su iya zuwa yin zabe ba, ba tare da jin tsoron kai farmaki ba, to an warware muhimman dangantaka da ke tsakanin gwamnati da jama’arta.
A cikin wata jihar, an kama wani mai sayen kuri’a da naira miliyan 25.9 da nufin sayan kuri’an mutane. A wani wuri, jami’an hukumomin zabe an same su da rashin gaskiya. Wannan ba kuskuren ne, ya kasance al’adar tsarin siyasa zabenmu a karkashin mulkin APC.
“Bayan shekaru masu yawa, gazawar yin amfani da na’urar tantance masu zabe (BBAS) a wasu jihohi ta sake haifar da tambayoyi game da kwarewar hukumar zabe. ‘Yan Nijeriya sun cancanci yin sahhin zabe mai ci da ke da gaskiya da amana a zukatan dukkan ‘yan kasa da kuma girmamawa daga sauran duniya. Hukumar zabe ba ta da wani uzuri na kin gudanar da sahihin zabe.
“Wannan zaben cike gurbi ya nuna wata alama da ake kokin haifarwa a lokacin zaben 2027. Idan tashin hankali, sayen kuri’a, tsangwama ga ‘yan takara da hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da jami’an zaben wajen yin rashin gaskiya, to ‘yan Nijeriya da al’ummar duniya ya kamata su shirya.
“Saboda haka, ADC tana kira ga Shugaba Tinubu ya aje ra’ayinsa ya gudanar da shugabanci na gaskiya ta hanyar tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya na iya jefa kuri’unsu tare da kwanciyar hankali da tsaro. Ya kamata Tinubu ya gane cewa babu wata gwamnati da za ta iya ikirarin samun sahihanci idan tana ci gaba da gudanar da zaben da ‘yan kasa da al’ummar duniya ke ganin sa a matsayin masu zamba.
“Muna kira ga INEC da ta gaggauta bincika dukkanin matsalolin da suka gudana na wannan zabe tare da hukunta jami’an da aka samu da laifin yin magudi, sannan ta dauki matakan gaggawa da suka dace don dawo da amincewar jama’a a cikin tsarin zabe na kasarmu. Idan har INEC ta kasa gudanar da zaben cike gibi, to ‘yan Nijeriya suna da hakkin bukatar hukumar da yi bayanin matsalolin da aka samu da kuma daukan matakai.
“Sannan kuma, ADC tana kiran ga al’ummar duniya, musamman abokan huldar dimokuradiyyar Nijeriya da masu sa ido kan zabe, ka da su yi shiru kan wannan zabe. Muna kira ga kungiyoyin al’umma da kafafen yada labarai da shugabannin addinai da duk wani dan Nijeriya da ke da ‘yanci da yaki da lalataccen. Idan ba mu kare tsarkin zabenmu ba yau, watakila ba za a samu wani abu da za a kare gobe ba.
“ADC tana sane cewa kotun Kanada ta bayyana PDP da APC a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’adda. Wannan dole ya zama abin kunya ga dukkan ‘yan kasa. Amma wannan zabe ya nuna karara kan wannan batu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp