Zaben Edo Da Ondo: ‘Yan Sanda Sun Ja Kunnen Masu Sha’awar Tada Tarzoma

Sufeto-janar na ‘yan sansa ya yi wa ‘yan siyasa da magoya bayansu gargadin cewa su bi doka kuma su guji duk abin da zai jawo tashin hankali. Gabannin zabukan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bayyana yiwuwar barkewar rikici, hare-hare daga abokan adawar siyasa, da kuma watsa bayanan karya a matsayin babban barazanar tsaro.

An shirya gudanar da zabuka a Edo da Ondo a ranar 19 ga watan Satumba da 10 ga watan Oktoba. Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu ya gargadi ‘yan siyasa da magoya bayansu da su kama kansu sosai ta hanyar bin doka.

Ya kuma shawarce su da su guji duk wani abu da ka iya kawo matsala a gudanarwar zabe a jihohin biyu. A wani jawabi daga kakakin ‘yan sandan, Frank Mba, ya ce shugaban rundunar ya yi gargadin ne bayan ya sake duba rahoton matsalar tsaro a zaben wanda kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin biyu suka gabatar a wani taro da aka gudanar a ranar Talata, 25 ga watan Agusta.

Exit mobile version