Akwai yiwuwar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Ahmad Lawan da tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio da Gwaman Jihar Sakwato, Aminu Waziri Tambuwal da sauran ‘yan takarar wadanda suka sa yi tikitin takara fiye da daya su fuskanci hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari a karkashin dokar zabe ta 2022.
Wannan furucin ya fito ne daga bakin Kwamishinan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Jihar Akwa Ibom, Mista Mike Igini a wata fira da ya gudanar tare da gidan talabijin Channels ranar Talata da ta gabata. Inda ya jingina hujjarsa da sashe na 115 (D) na dokar zabe ta 2022.
Ya kara da cewa, “Saboda haka duk wanda ya yi kuskuren sanya hannu ga fom din neman yin takara a yanki /shiyya ko na sakamako fiye da daya a lokacin guda, ya aikata laifi kuma wanda yana iya kai ga yanke masa hukuncin daurin shekara a kalla biyu gidan kaso.
Mista Igini ya yi karin haske kan abin da yake nufi da “yanki/ shiyya” a matsayin kalmar da hukumar zabe kan yi amfani da ita, wadda take nufin tsayawa takara biyu a lokaci guda, wanda ya hada da na shugaban kasa ne, na gwamna, sanata ko majalisar wakilai tare da na majalisar dokokin jiha.
A hannu guda kuma, ya ce duk dan takarar da ya yi wa wannan dokar hawan kawara zai fuskanci hukuncin daurin shekara biyu gidan yari. Ya ce dokar tana nan a sashe na 115 (3), wanda ta shafi hatta a jihohi ga masu yunkurin mallakar fam din takara guda biyu a lokaci guda, hakan yi wa doka karan-tsaye ne.
Ya ce Mista Akpabio ya tsaya takarar shugaban kasa ne a karkashin jam’iyyar APC, wanda daga bisani ya janye a ranar 7 ga watan Yuni tare da bayyana wa magoya bayansa su zabi Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya lashe zaben takarar shugaban kasa a APC.
Baya ga zaben fid da gwani na shugaban kasa, ranar 27 ga watan Mayu, Udom Ekpoudom, tsohon mataimakin safeto Janar na ‘yansanda, ya samu nasarar lashe zaben sanata a shiyyar arewa maso yammacin Jihar Akwa Ibom.
Shi kuma Sanata Lawan bayan ya sha kasa a zaben fid da gwani da jam’iyyar APC ta gudanar na shugaban kasa, wasu bayanai sun nuna ya nemi Bashir Machina, wanda ya samu nasarar lashe zaben arewacin Yobe ya janye masa.
Ya ce bisa hakan ya nuna cewa shugaban majalisar dattawan Nijeriya da Mista Akpabio wata kila a boye sun mallaki fom din takarar kujerar sanata a yankunansu, alhalin kuma a hannu guda suna neman takarar kujerar shugaban kasa.
Mista Igini bai tsaya nan ba, ya lissafo karin wasu ‘yan siyasar da suka bi ta kan wannan doka, wadanda suka hada da Gwamna Ben Ayade na Jihar Kuros Ribas, Tambuwal tare da Bala Mohammed na Jihar Bauchi.