Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya sha alwashin cewa zai yaƙi duk wani da ya yi satar dukiyar ƙasa idan ya zama shugaban ƙasa. Ya bayyana haka ne yayin da yake karɓar tawagar masu ruwa da tsaki daga jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin tsohon Sanata Idris Abdullahi.
Atiku ya ce lokaci ya yi da za a fuskanci matsalar cin hanci da rashawa da ƙarfi da kuma dakile barnar da ta hana Najeriya cigaba. Ya nuna takaicinsa kan yadda wasu ƴan ƙalilan ke hana ci gaban ƙasa saboda rashin tsoron doka da rashin shugabanci na gari. “Ya isa haka. Kowace ƙasa tana cigaba, amma mu a Najeriya muna tafiya baya saboda ayyukan wasu mutane kaɗan,” in ji shi.
- Atiku Da Wasu Sun Kafa Sabuwar Jam’iyya, Sun Nemi INEC Ta Musu Rajista
- Rasuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Afirka – Atiku
Ya ƙara da cewa dole ne a samu sauyi mai inganci wanda zai mayar da hankali kan jin daɗin talaka da gyaran tsarin gwamnati. A cewarsa, Najeriya na buƙatar shugabanni masu gaskiya, jajircewa da kishin ƙasa, ba masu cin gajiyar matsayi don aljihunsu ba.
Atiku ya ce hadakar shugabannin da ke ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC za su yi aiki kafada da kafada domin ganin an samar da sabuwar hanyar shugabanci mai inganci wadda za ta kawo sauyi ga rayuwar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp