Tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele ya sake shiga tsaka mai wuya kan zargin badakalan dala miliyan 6.
Rahotanni sun bayyana cewa binciken da aka gudanar sun tabbatar da cewa ana zargin tsohon gwamnan babban bankin da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da wawuredala miliyan 6.3 daga babban bankin Nijeriya lokacin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda aka yi amfani da sa hannunsa wajen fitar da wadannan makudan kudade.
A cewar rahotannin, an gano cewa an sace wadannan kudade ne a ranar 8 ga Fabrairun 2023, makonni kadan kafin zaben shugaban kasa, inda aka nuna cewa an yi amfani da wadannan kudade ne domin biyan masu saka ido kan zabe na kasashen waje.
A rahotannin dai suna zargin Mustapha tare da Emefiele wajen cire wadannan makudan kudade domin biyan masu saka ido kan zabe na kasashen ketare.
Rahoton bincike dai ya yi ikirarin cewa na’urar CCTB ta nadi yadda aka fitar da kudaden daga CBN.
Hakazalika, gwamnatin tarayya ta bukaci hukumar ‘yansandan kasa da kasa ta INTERPOL ta sanya idanu a kan wasu ‘yan Najeriya uku kan zargin yin takardun bogi.
Majiyoyi sun bayyana cewar ana neman wadanda ake zargin wani jami’in babban bankin Nijeriya, Odoh Ocheme da wasu mutane biyu ruwa a jallo ne a kan zargin kwaikwayar sa hannun tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammad Buhari domin satar fiye da dala milyan 6 da dubu 200 daga babban bankin.
Ana zargin Ocheme da kitsa almundahanar tare da yin takardun bogi da sunan Shugaba Buhari domin wawure fiye da dalar amurka milyan 6 da dubu 200 daga asusun babban bankin Nijeriya tare da Adamu Abubakar da Imam Abubakar.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa mai duke da sa hannun mukaddashin kwamishinan ‘yansanda kuma shugaban sashen kula da ayyuka da bincike na musamman a rundunar ‘yansandan Nijeriya, Oloho Okpoziakpo.