Daga Khalid Idris Doya, Abuja
Kwamitin nan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kafa domin bincikar hakikanin zargin da ake yi na cewar yara ‘yan kasa da shekaru 18 sun samu zarafin kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da ya guda a jihar Kano kwanaki, wanda hukumar zabe ta jihar Kano (KIDC) ta shirya, kwamitin ya kammala aikinsa hade da mika rahoton binciken da ya yi.
Kwamitin, kamar yadda bayanin ke kunshe a cikin sanarwar da Daraktar yadawa, fadakarwa da kuma ilmantar da jama’a na hukumar ta INEC Mr Oluwole Osaze-Uzzi ya sanya wa hanu gami da rabawa manema labaru a Abuja, ya ce kwamitin ya mika rahoton aikin da aka sanya shi ne wa shugaban INEC ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar Juma’a.
A lokacin da ke mika rahoton, shugaban kwamitin, Ahmed Nahuche, ya shaida wa shugaban INEC Mahmood Yakubu cewar sun yi zazzafar bincike gami da gayyatar dukkanin wadanda lamarin ya shafa zuwa gaban kwamitin domin bayar da bahasin abun da suka gani ya wakana a wajen zaben.
Wannan kwamitin dai INEC ce ta kaddamar da ita a watan Fabrairu da nufin ya binciko hakikanin zargin da ake yi na cewar yaran da basu kai shekarun kada kuri’a ba sun kada dauke da karin zabe a Kano.
Nahuche Ya ce, daga lokaci lokacin da suka amshi aikin sun gayyaci dukkanin wadanda abun ya shafa don tattaunawa gami da jin bahasi “wannan ganawar jin bahasin ta kunshi bangarorin kungiyoyin fararen huda, jam’iyyun siyasa, ‘yan jaridu na takarda da na na’ura, kungiyoyi ciki kuwa har da jami’an tsaro,”
“Kwamitinmu a sakamakon wannan ganawar da kuma gayyatar wadanda suka dace, mun samu hotuna, da kuma hotuna masu motsi, rahotonni, kundin adana, da kuma gabatar da bayanai daga wadanda abun ya shafa a jihar,”
“Nan da nan muka fara aikin ganowa da kuma binciken yadda aka gudanar da zaben kananan hukumomi na Kano wanda KASIEC ta gudanar,”
Ya ce “Kwamitin ya maida hankali wajen binciken hakikanin rahotonin da kafafen sadarwar zamani suka yada na hotona da hotuna masu motsi wadda ke cewa ana zargin yaran da basu kai munzalin kada kuri’a ba sun halarci wajen zaben kananan hukumomi a Kano, wanda wannan zancen ta tayar da kura sosai, don haka bincikenmu ya maida hakali kan wannan lamarin,”
“Hotunan mun yi musu dogon nazari a kansu, kwamitin nan ya tsaya sosai yak all hotunan da idon basira gaya,”
Nahuche ya kuma bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano da sauran jam’iyyun siyasa da su tabbatar da karfafar bin dokokin zabe domin gabbatar da ingancin da kuma bin hanyoyin da suka dace.
Ya bukaci jam’iyyun siyasa a kasar nan da su kasance masu yin ababen da zai kai ga samun ribar demokradiyya ba kokarin tarwatsa jin dadin shi demokradyyar ba.
Da ya ke amsar rahoton, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa Prof. Mahmood Yakubu ya jinjina wa kwamitin a bisa gudanar da aikin da aka daura masa, yana mai cewa hidimar da ta shafi harkar katin zabe abu ne wanda hukumarsu bata wasa ko kadan da shi don haka ne ya nemi jama’a da su ma su dauki lamarin da muhimmanci.
Idan dai baku mance ba, Bayan gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Kano ne dai wasu hotuna suka yi ta yawa na cewar ga yara kankana suna kokarin dangala kuri’a, wanda lamarin ta janyo ala tilas INEC ta kafa kwamitin bincike.