Abba Ibrahim Wada" />

Zidane Da Guradiola Sun Yabi Iniesta Bayan Ya Bayyana Aniyarsa Ta Barin Barca

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinadine Zidane ya aike da sakon fatan alkhairi ga Andres Iniesta kan kalaman sa na cewa zai bar Barcelona a karshen kakar nan, inda ya ce yana da yakinin cewa dan wasan ne yakamata a ce ya lashe kyautar Ballon d’Or a shekarar 2010.

Fitaccen dan wasan tsakiyar wanda ya lashe kofin laliga har sau 8 dana zakarun Turai 4 amma bai tada samun lambar yabon dan wasa mafi hazaka ba, a ranar Juma’a ne ya sanar da aniyarsa ta barin Barcelona.

Ko da ya ke dai Iniesta mai shekaru 33 bai sanar da Club din da zai koma ba, amma ana ganin yana shirye-shiryen komawa wata kungiyar kwallon kafa da ke China ne.

A shekarar 2010 ne dai yakamata a ce Iniesta ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya  amma Lionel Messi ya shige gabansa.

Shi ma dai mai koyar da yan wasan Manchester City Pep Guardiola a na shi sakon taya murnar cewa ya yi tarihi ba zai taba mantawa da rawar da Iniesta ya taka a Barcelona ba cikin kusan shekaru 22 da ya yi.

Da ma dai a karshen kakar nan ce ake saran Iniesta zai sanar da ritayarsa da ka bugawa kasarsa kwallo bayan kammala gasar cin kofin duniya da za ta gudana a Rasha.

 

Exit mobile version