Ƙungiyar ‘yan jaridu a shiyyar Arewa maso gabas ƙarƙashin jagorancin mataimakiyar shugabar shiyyar Hajiya Aisha Ibrahim Kwaya ta kai ziyarar gani da ido zuwa yankin Mambilla da wasu sassa na Jihar Taraba, don gane wa idonsu irin albarkatu da rayuwar jama’ar yankin. Tafiyar ta ƙunshi shugabanin ƙungiyar ta NUJ da Sakatarorinsu da kuma wasu ƙalilan daga cikin ‘yan jaridun shiyyar.
Wakilinmu MU’AZU HARƊAWA daga Bauchi ya kasance cikin tawagar, a dalilin haka ya naƙalto wa masu karatu yanayin yankin na Mambila, wanda ya ke da damina biyu saboda yadda ake ruwan sama na watanni goma, kuma wurin a kullum yana cikin ni’imar sanyi ne, dalilin da ya sa mutanen yankin ba sa aiki da fanka ko na’urar sanyi a yawancin lokuta. Haka kuma babu yawan cututtuka ko ƙwari kamar su sauro da cinnaka, ƙudaje da sauransu a wannan waje. Kuma sun fi yin safara da Babura don hawa tsaunukan yankin har zuwa cikin ƙasar Kamaru.
Tafiyar awa goma ce daga garin Jalingo zuwa Gembu cikin ƙaramar hukumar Sardauna mai nisan kilomita 600, wannan tafiya ana yin ta a yanayin da ke bayar da sha’awa ga maziyarta tamkar mutum ba a Nijeriya yake ba. Kuma zamantakewar yankin tana da kyau sosai Allah ya albarkaci wajen da harkokin kasuwanci da noma da dabbobi da tuddai masu ban sha’awa da ke iya birge duk wanda ya je wajen.
Tun daga garin Serti da ke ƙaramar hukumar Gashaka zuwa Maisamari har zuwa Nguroje zuwa Kakara zuwa Gembu tafiyar sama da kilomita 200 ce kan duwatsun tsaunukan Mambila lamarin da sai wanda ya gane wa idonsa. Tafiyar kwalta ce amma wani wajen hanya ba kyau wani wajen kwanoni ne irin na mutuwa ga wanda ya zo da tuƙin ganganci, haka kuma idan dawowa ake yi shi ma sai motar da birkinta ke da kyau kafin ta iya gangarewa lafiya. Kan hanyar zuwa ko dawowa ana samun motoci masu yawa sun lalace a hanya duk da cewa kowane mai abin hawa sai ya yarda da lafiyar motarsa kafin ya hau waɗannan tsaunuka, amma kuma babu yawan hatsari a hanyar kowa cikin natsuwa ke tafiya saboda kowa ya san idan ya bar hanya zai faɗa cikin rami mai zurfi sosai wanda zai kasance mutuwa kusa.
Garin Gembu na da girma sosai a tsakanin tsaunuka suke zaune, kuma tsarin rufin gidajen kamar na garin Ibadan yake saboda yawan ruwa da yanayi mai sanyi da suke da shi ya sa rufin kwanukan yankin sun yi ja, yawancin gidajen suna cikin kwari ne da tsaunuka. Waje ne da ke kan iyaka da ƙasar Kamaru, saboda bai wuce Kilomita biyu ba daga garin Gembu idan an haura wassu tsibirai sai a shiga yankin Sardauna da ke cikin ƙasar Kamaru. Wuri ne wanda ke da yanayin noma da kiwo, suna noma duk wani nau’i na abinci da kuma
bishiyoyi kala-kala masu ban sha’awa da suka ƙunshi mangwaro da gwaiba da tuffa da fiya da koko da kwakwar manja da ganyen shayi da doya da dankali da katako mai yawan gaske da ake fita da shi mota-mota, kuma kayan abinci ba tsada a wannan waje. Haka kuma akwai kamfanin sarrafa ganyen shayi na Highland tea wanda idan da an gyara gonakin yadda ya kamata za a ci moriya har a wadata dukkan ƙasashen Afirka da wannan ganyen shayi, kamar yadda manajan kamfanin Malam Ibrahim Nunuji ya bayyana.
Yanayin Mambilla waje ne mai sanyi a kowane lokaci, idan ana zafi a arewacin Nijeriya su kuma sanyi ake yi, don haka farkon abin da mutum zai fara ba ka idan ka ziyarce shi shayi ne mai zafi. Haka kuma duk gidan da ka je za ka samu sun tanadi bargunan amfaninsu da na baƙin da suka ziyarce su don a kowane lokaci yanayin yana da sanyi musamman tsakiyar dare. Haka kuma duwatsun da ke yankin cike suke da farin gajimare wani lokaci kuma raɓa na zubar da sanyi har da dusar ƙanƙara. Suna samun ruwa na watanni tara zuwa goma a shekara, yawanci sau biyu suke shuka amfani a gonakinsu saboda ni’imar yankin. Wannan dalili ya sa masu fanka ko na’urar sanyi ba su da kasuwa a yankin, saboda akasarin gidajensu ba sa amfani da su don samun iska. Hatta Otel da na zauna babu fanka babu Aircondition a ɗakin. Kuma garin Gembu da sauran yankuna da ƙauyukan yankin ba sauro ba ƙudaje ko ƙwari irin su cinnaka da zago da makamantansu sai ɗan abin da ba a rasa ba. Ɗakunan otel a wajen kuma ba sa wuce Naira dubu biyu zuwa dubu biyar kwana guda. Allah ya albarkaci yankin da matasa masu dogara da sana’ar noma da kiwo da acaɓa, saboda motoci ba su cika hawa tsaunuka ba sai Babura, don haka gwamnati da ‘yan siyasa ko ‘yan kasuwa ke kawo Babura masu yawa don raba musu kyauta ko rance. Kuma waje ne da suke haɗe kirista da Musulmi kusan kowane gida a garwaye ake amma ba mai ƙyamar wani kowa yana addininsa yadda yake so.
A lokacin da ake fama da dokar ta – ɓaci a jihohin maƙwabtan Taraba, wannan yanki ba su san ana wata rigima ba kowa yana gudanar da harkokinsa ba matsala. Ofisoshin ‘yan sanda da gidajen yari ba su san a cika buhu da yashi a rufe hanya ba, jami’an tsaro ba sa damun mutane kamar yadda yake faruwa a wasu Jihohin Arewa. A taƙaice duk abin da ke faruwa a Arewa wannan yanki suna ji ne kurum a kafafen labarai kowa yana harkokinsa yadda ya kamata babu tsangwama. Kuma hanya ɗaya ce tak ta shiga zuwa Gembu daga ko’ina sai hanyar tsaunuka da ta ƙetara zuwa Kamaru, don haka ko mai aikata laifi ya shiga yankin dole ya sha wahala kafin ya samu mafita zai iya shiga hannu.
Game da cututtuka kuma babu Polio da sauran cututtuka masu damarwa saboda akwai yanayi mai kyau kuma ba ƙazanta a yankin, kowa ka gani a yankin Mambila mutane da dabbobi a ƙoshe suke babu alamun yunwa a jikinsa, haka babu yawan mabarata kamar yadda ake samu a wasu garuruwa. Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Sardauna Dokta Jedua Daɓid ya bayyana min cewa suna da matsalar cutar ƙanjamau saboda waje ne da ke kan iyaka, don haka suka samu haɗin kan wani Baturen Kanada mai suna Rebaran Arthur G. Helwig suka buɗe cibiyar musamman mai suna Gembu Centre for HIƁ/AIDS suka duƙufa wajen ƙoƙarin shawo kan cutar ta hanyar gwaji da bayar da shawarwari, don haka yanzu an samu shawo kan wannan matsala ta ragu sosai.
Wani matashi a yankin mai suna Joɓita Shafe, ya bayyana min cewayankinsu ba a taɓa samun rikici ba, idan baicin wanda ya auku watannin baya sakamakon rashin kishi na wasu marasa son zaman lafiya da suka tayar da rigimar ƙabilanci da addini wanda suke fatar Allah ya sa ƙarshen wannan matsala ke nan har abada. Ya ce kuma matasa na dogaro da
Kansu yadda ya kamata. Koda idan harkokin siyasa sun zo matasan suna gudanar da komai cikin tsabta da wayewa ba a samun yawan tashin hankali duk da irin yawan ƙabilu da ake da su a wajen akwai Kirista da Musulmi har da masu addinin gargajiya duk a haɗe ake amma babu matsala saboda tun da aka naɗa sarki a Gembu sai aka magance duk wata matsala ta tashin hankali.
Halin da ake ciki kuma mutane na ruruwar zuwa yankin don auro mata suna sauƙo da su zuwa jihohin Arewa saboda irin ladabi da iya zama da miji da matan yankin ke da shi. Bayan haka kuma auren babu tsaraba da yawa saboda akwai waɗanda ke zuwa jihohi da hotunan ‘yan mata idan an gani a kan je can a daidaita a biya sadaki idan an amince da juna ana iya ɗaura aure nan take a ba ango kuɗin sayen kayan ɗaki ya zo ya saya wa matarsa. Idan iyaye ba su da ƙarfi kuma sai ya ɗauko matarsa ya zo ya saya mata abin da yake so su ci gaba da zama.
Garin Gembu shi ne Helkwatar ƙaramar hukumar Sardauna, suna da kayan more rayuwa irin na zamani waɗanda suka ƙunshi makarantu da asibitoci da hanyoyi na kwalta da layukan sadarwar Salula irin na zamani. Haka kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suna zuwa wannan yanki suna gudanar da ayyuka lamarin da ya sa ake samun Turawa a yankin, saboda akwai zaman lafiya da girmama juna da ingancin rayuwa. Don haka akasarin shugabannin da suka mulki Nijeriya suna da filaye a wannan yanki, sun kewaye mutanen wajen suna aro don noma da kiwo. Kuma akwai ƙananan jirage masu saukar ungulu da suke safarar mutane daga garin Jalingo zuwa wannan yanki saboda masu kai ziyarar yawon shaƙatawa ko harkokin
kasuwanci.
Farashin kayayyakin masarufi da man fetir da sauran abubuwa kamar sutura ya ɗan ɗara na sauran garuruwan Nijeriya a farashi saboda irin wahalar da ake sha kafin a haura da su zuwa yankin. Amma kuma ba irin kayan da babu a wannan yanki na Nijeriya da na ƙasashe renon Faransa saboda shigo da su da ake yi daga cikin ƙasar Kamaru, kuma farashin
bai hau sosai ba don za ka iske kowane talaka yana iya sayen abin da yake buƙata daidai ƙarfinsa, illa a wannan lokaci da matsalar fatara ta dami mutane.
Da jimawa gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar gina babban Otel da filin jirgin sama da hanya a yankin Mambilla. Kuma za a gina babbar madatsar ruwa wacce za ta samar da hasken lantarki da zai amfanar da dukkan shiyyar Arewa maso -gabas kuma akwai fatar idan har shirin da gwamnatin Taraba da ta Tarayya suke yi kan yanki ya tabbata za a samu ci gaba wanda jama’a ba sa zato a yanki. Haka kuma za a inganta samar da kayan more rayuwa don jan hankalin masu zuba jari ta yadda za a mayar da yankin ya riƙa karɓar masu zuwa yawon shaƙatawa daga ko ina a duniya. Haka daga cikin Nijeriya akwai buƙatar dukkan masu son hutawa su riƙa ziyartar wannan yanki saboda akwai gandun yawon shaƙatawa na ƙasa da ke Gashaka, kuma akwai dabbobi da kayan tarihi da mutane za su buƙaci gani don ɗebe kewa. Haka kuma akwai harkokin kasuwanci da sauran wuraren da mutune za su ziyarta don hutawa da samun ingancin rayuwa har zuwa lokacin da kowa zai buƙaci komawa inda ya
fito.
Sai ko ganin yadda a kwanakin baya aka samu rikici wanda ya shafi ƙabilanci da addini tsakanin Fulani da ‘yan ƙabilar Mabilla, wanda ya ci rayukan mutane masu yawa har ma da dabbobi da gidaje da dukiyoyi, akwai buƙatar gwamnati ta tashi a tsaye domin hukunta dukkan waɗanda suka yi sanadiyyar wannan rigima domin guje wa abin da ka iya faruwa a
gaba na ɗaukar fansa da makamantansu. Saboda yanki ne da aka san shi da zaman lafiya da kuma harkar arziki amma wasu mutane suna neman lalata martabar yankin.
Da fatar gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Taraba za su ci gaba da kare martabar wannan yanki ta hanyar inganta zaman lafiya tare da taka wa jami’an tsaro birki saboda yadda suke tsare mutane suke hana su shiga wasu yankunan Jihar Taraba har sai sun biya kuɗi na cin hanci kai ka ce wata ƙasa za su shiga. Alhali wannan gwamnati na iƙirarin tana yaƙi da cin hanci da rashawa lamarin da ya zamo tamkar yaudara a halin da ake ciki. Don haka ya kamata a sanya ido kan jami’an tsaron soja da ‘yan sanda da sauran masu kayan sarki domin dawo da martabar wannan yanki da aka sani da zaman lafiya wato Mambilla.