A wani yunkuri na karfafa hulda da abota tsakanin Sin da Nijeriya, jiragen sojin ruwan kasar Sin 3, sun isa Legas na Nijeriya a jiya Litinin, da zummar karfafa tsaron teku a yankin.
Zan iya cewa, wannan ziyara ce ta karfafa tsaron teku bisa la’akari da zuwanta a kan gaba, wato watanni 6 bayan Nijeriya ta kaddamar da tashar jiragen ruwa mai zurfi dake Lekki na jihar Lagos, wanda ke zama wata katafariyar hanyar bunkasa cinikayya da bunkasa tattalin arzikin kasar, da ma jan hankalin karin masu zuba jari daga ketare. Har ila yau, ba za a taba raba nasarar kafuwar wannan katafariyar tasha da tallafin kasar Sin ba, lamarin dake kara nuna amincin dake tsakanin Sin da Nijeriya da ma yadda kasar Sin din ke da kwarin gwiwa kan ci gaban Nijeriya. Wannan ya sake bayyana matsayin Sin na aminiyar dake ingiza ci gaban ’yan uwanta kasashe masu tasowa.
A matsayinta na irinta mafi girma a yankin, tabbatar da ganin cikar burin kafa wannan tasha da dimbin alfanun dake tattare da ita, na matukar bukatar tsaro. Dole ne batun tsaro ya zama a kan gaba bisa la’akari da yadda yankin ke fama da matsalar fashin teku. Tabbatuwar tsaro ita ce za ta kai ga samun kyawawan sakamakon da ake buri.
Sin tana da gogewa ta fuskar tsaro a cikin gida da ma iyakokinta, har da ma sauran sassan duniya da take aikin tabbatar da zaman lafiya, yayin da Nijeriya ke fuskantar matsaloli daban-daban a bangaren, kuma fashin teku na daya daga cikinsu. Muna sa ran ziyarar kwanaki 5 ta jirage da sojojin ruwan Sin a Nijeriya, za ta inganta samar da hanyoyin shawo kan matsalar fashin teku da ake fuskanta a Nijeriyar, wanda ke kai wa ga garkuwa da baki ’yan kasashen waje domin neman kudin fansa ko ma asarar rayuka da dukiyoyi.
Duk da cewa masharhanta na ganin wannan lamari ba zai yi wa kasashen yamma dadi ba, ba shakka Nijeriya da ma yankin yammacin Afrika, na bukatar tallafin tsaro da duk wani yunkuri da zai tabbatar da kwanciyar hankali da gudanar da al’amura yadda ya kamata, kuma kasar Sin ta nuna cewa a shirye take ta share musu hawaye.
Dole kasar Sin ta ci gaba da samun karbuwa a tsakanin kasashe masu tasowa, musamman ma na Afrika, domin ta nuna ta damu da yanayin da suke ciki, kuma tana iyakar kokarinta na ganin ta samar musu mafita cikin ruwan sanyi kuma bisa adalci da girmamawa. Don haka, wannan ziyara ta zo a kan gaba, domin za ta amfanawa Nijeriya da ma sauran kasashen yankin yammacin Afrika.