ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Bindiga Sun Kashe Wani Malamin Makaranta Da Wasu Mutum 2 A Sakkwato

by Abubakar Sulaiman
2 days ago

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kashe wani sabon malamin makaranta da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ɗauka aiki, Maniru Sa’adu Imam mai shekaru 30, tare da direban motarsu, Abdurrahman Umar, da ɗansa mai shekaru biyar, Abubakar Abdurrahman, a kan hanyar Gundumi zuwa Isa. Lamarin ya auku ne da yammacin ranar Laraba, 21 ga watan Oktoba, 2026, yayin da mamatan ke kan hanyar komawa gida Ƙaramar Hukumar Isa bayan sun kammala aikin tantance albashin sabbin malamai a birnin Sakkwato.

Bayanai sun nuna cewa sakamakon ƙalubalen tsaro a yankin, mazauna Isa na tafiya birnin Sakkwato ne sau biyu kacal a mako—ranakun Laraba da Asabar a ƙarƙashin rakiyar dakarun tsaro.

Wani shaidar gani da ido, Malam Kabiru Isa, ya bayyana cewa motar mamatan ta yi jinkirin tashi tare da tawagar da jami’an tsaron ke yi wa rakiya da misalin ƙarfe 4:00 na yamma. Yayin da tawagar ke tafiya a kusa da Gundumi, jami’an tsaron sun yi arangama da ƴan bindiga tare da korar su da harbe-harbe, amma daga bisani maharan suka sake dawowa suka yi wa motocin da ke biye a baya kwanton-ɓauna.

ADVERTISEMENT

Maharan sun buɗe wuta kan motar, inda suka kashe mutanen uku nan take tare da jikkata wasu fasinjoji uku, yayin da fasinja ɗaya kuma har yanzu ba a san inda yake ba. Marigayi Imam, wanda ya bar mata ɗaya da ɗa guda, an tura shi koyarwa ne a makarantar sakandare ta GDSS Maitandu, inda ko albashinsa na farko bai karɓa ba kafin wannan kisan gilla. An dai gudanar da jana’izar mamatan ne a safiyar ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, a garin Isa cikin matsanancin jimami da kuka.

Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar Ƴansandan Jihar Sakkwato ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, yayin da ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, bai samu nasara ba sakamakon rashin ɗaga kiran waya.

LABARAI MASU NASABA

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

Wannan sabon hari ya sake fito da irin mummunan halin fargaba da matafiya ke fuskanta a kan hanyar Gundumi zuwa Isa a gabashin Jihar Sakkwato, wadda ta daɗe tana zama babbar maɓoyar ƴan bindiga.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
  • Abubakar Sulaiman
    Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

MASU ALAKA

ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai
Manyan Labarai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume
Manyan Labarai

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu
Manyan Labarai

Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

October 24, 2026
Next Post
Doguwar Tafiya A Sabon ZamaniZuwa Afirka Da Ke Kan Hanya

Doguwar Tafiya A Sabon ZamaniZuwa Afirka Da Ke Kan Hanya

LABARAI MASU NASABA

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

October 24, 2026
Ya Kamata A Baiwa Muryoyin Kasashe Masu Tasowa Damar Sauraro

Ya Kamata A Baiwa Muryoyin Kasashe Masu Tasowa Damar Sauraro

October 24, 2026
Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

October 24, 2026
Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

October 24, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.