Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta yi nasarar daƙile yunƙurin wasu da ake zargin ƴan daba ne na kai farmaki gidan Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar.
A cewar kakakin rundunar ƴan sandan, SP Abdullahi Kiyawa, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 31 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 6 na yamma a mahadar Chiranchi da ke karamar hukumar Gwale.
- Kikikakar Masarautar Kano Tsakanin Sanusi Da Aminu…
- ‘Yansanda Sun Karyata Jita-jitar Kai Harin Garkuwa Da Mutane A Jami’ar BUK
Rahotanni sun ce ƴan daban ɗauke da muggan makamai sun yi ta jifan mutane da duwatsu tare da yunƙurin shiga gidan shugaban jam’iyyar.
Cikin gaggawa tawagar jami’an ƴansanda reshen yankin Gwale ya daƙile harin tare da dawo da zaman lafiya a yankin.
Ko da yake babu wani da aka kama, amma rundunar ƴansandan ta bayyana faruwar lamarin a matsayin rikici tsakanin wasu ƴan daba guda biyu, inda ta bayyana sunayensu da Abdul’Yassar Alias Jonny da Birbiri, da Jinjiri Aljan a matsayin waɗanda suka shirya ta’asar.
A halin yanzu dai ana ci gaba da kokarin kamo waɗanda ake zargin, tare da ƙara tsaurara tsaro a yankin domin hana tada zaune tsaye.