Connect with us

RAHOTANNI

A Wane Yanayi Dino Melaye Ke Ciki A Hannun ’Yan Sanda?

Published

on

Bayanan da su ke fitowa daga bangaren rundunar ’yan sandan Nijeriya na nuni da cewar rigimammen dan majalisar dattawan nan, Sanata Dino Melaye, wanda ya mika mu su kansa a ranar Juma’a ya na nan cikin yanayi mai kyau, bayan ja’inja a tsakaninsu na tsawon kwanaki.

A ranar Juma’a ne Sanata Melaye ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan kasar bayan ta girke jami’anta masu dimbin yawa fiye da mako guda su na yi wa gidansa kawanya da shan rantsuwar sai sun cafke shi.

A wata sanarwar da babban jami’in da ke magana da yawun rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Jimoh Moshood, ya aike wa manema labarai, ta ce, a na cigaba da gudanar da bincike a kan dan majalisar kuma da zarar an kammala za a mika shi gaban kotu.

‘Yan sandan su na zargin dan majalisar ne da yunkurin kashe wani jami’in dan sanda mai suna Danjuma Saliu a ranar 19 ga Yuli, 2018. Sai dai ya sha musanta zargin da cewar sam babu hannunsa.

Mista Moshood ya ce an girke ‘yan sanda a kofar gidan Sanata Melaye ne saboda ya ki amsa gayyatar da su ka yi ma sa, domin ya yi bayani kan zargin yunkurin kisan kan da a ke yi ma sa.

Da ma Sanata Dino Melaye ya sha cewa, ya ki mika kansa ga rundunar ‘yan sandan ne saboda zargin za su yi masa allurar mutuwa, ko da ya ke ‘yan sandan sun musanta zargin nasa.

Ranar Laraba ne rundunar ‘yan sandan ta girke na’urar toshe sadarwa a kofar gidan Sanata Dino Melaye.

Hakan ba ya rasa nasaba da wani sakon Twitter da ya wallafa a safiyar Larabar, wanda ya ke nuni da cewa, ‘yan sandan su na kawo kayayyaki, domin su fasa kofofin shiga gidansa.

Kodayake, tun kafin Dino ya mika kansa ga ‘yan sandan Nijeriya, ya shigar da wata kara a gaban babban kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta hannun lauyansa, Nkem Okoro na cambar Mike Ozekhome (SAN), inda ya nemi kotun ta tilasta wa ‘yan sanda barin gidansa da janye dukkanin shingayen da su ka kakaba a wajen.

A ranar Alhamis ne dai kotun ta yi zamanta kan takardar bukatar janyewar ’yan sandan da kuma bukatar tabbatar ma sa da ‘yancinsa na dan adamtaka da ya shigar a gaban kotun. Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar ta Sanata Melaye. Don haka wasu na garin rasa samun mafaka da ya yi a kotun ne ya sanya shi mika kansa, domin ya rasa wata madogarar kamawa.

A wani bari na takardar Dino, ya roki kotun da ta shiga tsakani hadi da bayar da umurni mai karfi da zai tilasta wa ‘yan sanda tattara ya-nasu-ya-nasu su bar ma sa gidansa hadi da kwashe dukkanin wani shingayen da su ka kakaba a gaban gidan nasa domin neman baiwa iyalansa da abokan siyasarsa damar ganawa da shi cikin aminci.

Har-ila-yau, ya kuma nemi kotun ta bayar da umarnin hana ‘yan sandan Nijeriya cigaba da neman rayuwarsa da kuma hana su jefa ma sa firgici da razani a cikin rayuwarsa. Kana, ya kuma nemi kotun ta hana ’yan sanda cigaba da neman cafke shi da cakumo shi, har sai an kammala sauraron karar da ya shigar a gaban kotun.

A gefe guda kuma, alkalin kotun, Mai shari’a N.E. Maha, ta ki amincewa da bukatar da Dino Melaye a gabatar ma ta da kuma umartar a cigaba da sauraron shari’ar a haka nan.

Kawo yanzu dai, Sanata Dino ya na garkame a hannun ‘yan sanda, inda su ka shaida cewar su na kan bincike idan su ka kammala za su kai shi kotu.

Duk da bayanin da ke fitowa daga bangaren ‘yan sanda na cewar Dino Melaye ya na cikin yanayi mai kyau, amma a faifen bidiyo da a ke tsammanin ’yan sandan ne su ka saki a kafafen sadarwa ya nuna tun daga fitowar Dino Melaye daga gidansa a jirkice ya ke, inda hoton mai motsi ya nuna Dino cikin wani yanayi kamar na tausayi, har fitowarsa da shigarsa ofishin ‘yan sandan a daddafe ya yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!