Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Iyalin Mutumin Da Ya Mutu A Ofishin NSCDC Sun Koka

Published

on

A ranar Talata ne iyalan Razak Ahmed, sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnar Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, da su binciki kisan dansu wanda ya mutu a hannun hukumar NSCDC reshen Jihar Ondo. An bayyana cewa, jami’an hukumar NSCDC ne suka cafke Razak ranar Lahadi, bisa laifin fade.
Ana zargin mamacin da yi wa diyarsa mai shekara 12 fade a yankin Aule da ke Akure. “Daya daga cikin yarinyarsa na dayar matarsa ce ta kai rahoton lamarin ga ofishin hukumar NSCDC da ke Akure ranar Lahadi, jami’an hukumar NSCDC sun buge shi har sai da ya mutu a ranar Talata,” in ji majiyarmu.
Kanuwar mamacin mai suna Misis Taiwo, bayyana cewa an bugi Razak da sanda har sai da ya mutu. Ta ce, “Daya daga cikin ‘ya’yansa ne ta kai kararsa ofishin hukumar NSCDC, inda suka cafke shi, sannan suka garzaya da shi ofishinsu.
“Jami’an hukumar NSCDC sun fara bugun shi da sanda lokacin da ya bayyana musu cewa bai aikata laifin da ake zargin da shi ba. Jami’an hukumar NSCDC sun azabtar da shi har sai da ya mutu, sannan suka dauki gawar zuwa asibiti.”
Taiwo ta bukaci gwamnati da kuma kungiyoyin kare hakkin bi’adama da su taimaka wa iyalan wajen samun adalci, ta kara da cewa hukumar NSCDC tana kokarin rufe lamarin.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi wajen jin ta bakin kakakin hukumar NSCDC, Mista Samuel Oladipo, amma abin ya ci tura domin bai dauki wayar da ya buga masa ba, sannan kuma bai maida sakon wasikar da ya tura masa ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!