Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Neja Ta Amince Da Sake Bude Masallacin Farin Doki

Published

on

Sakamakon wani rikicin bangarancin addini da ya taso a Farin Doki a kwanakin baya da ya janyo rufe wani masallacin da ya shekara sama da sittin ana sallah a cikinsa yasa hukumar kula da harkokin addinai a jihar Neja bisa jagorancin Dokta Umar Faruk Abdullahi ta umurci garkame masallacin.

Bayan wani zama da hukumar tayi da sarakunan gargajiyar garin wanda ya kunshi dagaci da sarkin Hausawa, har da mai unguwar yankin da shugabannin bangarorin da ake rikicin, zaman ya amince da sake bude masallacin da cigaba da ayyukan Ibadah tare da nada limamin da zai cigaba da jagorantar sallah da na’ibinsa har ladanin da zai rika kiran sallah.

Da yake karin haske ga wakilin mu bayan wani zama da hukumar tayi na kusan awanni biyu zuwa uku, shugaban yace wata rigima ce ta taso akan wanda ke da hakkin kula da masallacin tsakanin ‘yan Izala da ‘yan Darika wanda ta kai ga har an dauki lauyoyi, inda suka rubutawa kwamishinan ‘yan sanda shi kuma ya turawa maigirma gwamna inda shi kuma gwamnan ya umurci mu shiga cikin lamarin, yau din nan Allah Ya ba mu ikon daidaita su kuma kowa ya amince da tsarin da muka bullo da shi.

Zaman da muka yi da dukkan bangarorin duk sun amince da limancin Malam Sulaiman daga bangaren Izala, sai kuma ni’ibinsa daga bangaren Darika yayin da shugabannin garin suka nada sabon ladan wanda kowa ya amince kuma ya gamsu. Kuma mun yarda da cewar a lokuttan sallah a hadu a tsakiya kamar sallar azahar za a kira sallah daya da kwata sai ayi sallah karfe daya da rabi, yayin da la’asar da sauran salloli ba bu wata gardama a ciki. Sannan tsakanin sallar magriba zuwa isha’i an baiwa ‘yan Darika damar yin wazifa na minti talatin inda za a bada tazarar minti goma kafin sallar Isha’i. Kowani gefe dai sun amince da wannan tsarin.

Dan haka muna kiran al’ummar musulmi na Farindoki da jiha gaba daya, zama lafiya yana da muhimmanci, yafi duk rigimar nan da ake yi akan sallah. Kar kowani gefe yaje yace yana buki dan farin cikin shi ne yayi nasara dukkanin bangarorin kowa yayi nasara domin ana zama ne bisa tafarkin koyarwar addini. Dukkanin al’ummar Farindoki ‘yan Izala da ‘yan Darika kowa ya samu nasara muddin aka samu zaman lafiya.

Muhammed Dagna wanda mahaifinsu ya gina masallacin sama da shekara sittin da biyar da suka gabata yace yau sun amince tunda yanzu an ce masallacin na hannun gwamnati kuma kayan Allah ne sun amince da wannan sakamakon wannan zama kuma da zaran ya koma zai nemi ‘yan uwansa da ake rigimar da su gaban dagaci domin ya kara jaddada masu matsayar gwamnati akan wannan lamari, abinda yasa tun farko neman su karbe masallacin a matsayin gado tunda mahaifinsu ya bada fili kuma ya assasa masallacin duk da bai raye a halin yanzu ba sa son kan wannan lamari ayi tashin hankali, kuma malamai da ita gwamnatin jiha ta nuna mana cewar wannan matsayin na gadon masallacin kuskure ne babba kuma mun gamsu da wannan matsayin da aka dauka yau talata 9 ga wata bakwai na shekarar 2019. Inda aka ce Malam Sulaiman zai jagoranci sallah a masallacin nan, yayin da Malam Abdullahi Abdulkarim zai zama na’ibinsa, sai Malam Isma’ila Dahibe zai zama ladan, wanda ake wadannan mutanen uku su kadai aka amince da su cigaba da jagorantar wannan masallacin.

Hukumar mai kula da harkokin addinai dai ta amince da cigaba da yin sallah nan take, wanda kuma sarakunan yankin da masu fada a jin yankin zasu cigaba da sanya idanu dan gujewa faruwan hakan a gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: