Connect with us

LABARAI

Lamidon Adamawa Ya Shawarci Shugabanni Da Su Gujewa Kalaman Batanci

Published

on

Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo, ya gargadi shugabannin da suka gabata da na yanzu da su kiyayi kalaman batanci wanda ka iya jawowar tarwatsewar kasarnan. Barkindo ya bayyana hakan ne a sakon Idin sallar Layya da ya gabatar a birnin Yola a ranar Lahadi.

Basaraken ya nuna takaicinsa na yadda wadansu shugabannin da suka gabata da na yanzu da shugabannin addini suke rura wutar rikici ta hanyar kalaman na su, inda ya ce tabbas hakan abin damuwa ne. Ya kara da cewa; abin takaici ne a ce kalaman batanci na fitowa ne daga shugabannin da ya kamata a ce sun hade kan al’umma ne. Ya ce akwai bukatar a kiyaye kalaman da za a rika furtawa, domin kuwa yana da hadarin gaske. Ya ce kasar Rwanda da Burundi abin misali ne.

Har wala yau Basaraken ya nuna damuwarsa na yadda ake garkuwa da jama’a a kasarnan tare da kashe-kashen ba gaira ba dalili na mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, sannan ya nuna takaicinsa bisa yadda matasa ke fadawa harkar shaye-shaye. Ya ce yanzu hatta matan aure sai ka samu suna shaye-shaye. Inda ya yi kira ga gwamnati da ta tallafawa hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi wato NDLEA domin yaki da wannan dabi’a.

Ya ce ya baiwa Hakimai da masu Unguwanni da suke karkashinsa da za su hada hannu da hukumar NDLEA din wajen yaki da shan miyagun kwayoyi ta hanyar bayyana duk wani abu da ba su yarda da shi ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: