Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa da ke yankin kudu ta nuna takaicinta kan halin ko-in-kula da gwamnonin arewa suke yi wa al’umma tare da nuna yunwansu a fili wajen ci gaba da zama a karagar mulki a 2023, wanda hakan ne ya nuna cewa babu shugabanni masu kishi a arewa.
Gamayyar Kungiyoyin Matsan Arewa da ke Kudancin Nijeriya a Jihar Legas ta kuma bukaci al’ummar arewacin Nijeriya su zabi cancanta su manta da batun biye wa jam’iyya a zaben 2023.
Shugaban gamayyar kungiyoyin matasan arewa a kudu, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci shi ya bayyana hakan a madadin ‘ya’yan kungiyar a wata sanarwar manema labarai da ya aike wa wakilinmu.
A cewar gamayyar, ta yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kyakkyawan zato da fatan alkairi a zaben shekarar 2015, wanda har ta dunga sayen katin tana tura masa kuadade domin ya samu damar darewa a kan karagar mulki, amma kuma a halin yanzu dai arewa ta zama kushewa, inda ake ta kashe al’umma ba ji babu gani duk ka cewa dan arewa yake shugabancin kasar nan.
“Shugabanninmu na arewa su sani Allah ba ya zalunci, sannan kuma ba ya barin duk wani azzalumi a doran kasa, da yana bari ai da har yanzu Fir’auna na nan a doron kasa.
“Domin haka muna kira ga matasa da su guji bangar siyasa, domin babu ribar da za su samu. Wadanda ma suke yi wa bangar siyasar suna ganin ‘ya’yansu a wurin bangar siyasar, don haka wannan ya isa mai hankali ya yi karatun ta-natsu.
“Ana yi wa arewa mugun tanadi kuma wadanda ake ganin ya kamata su yi magana da su ma ake hada baki wajen yakarmu.
“Akwai arziki a yankin arewa mai dinbin yawa, tun daga kan zinari da lu’u-lu’u da sauran manyan ma’adanai, wanda shi ne dalilan da ya sa ake kashe mu, amma kuma a guji fushin takala, domin a halin yanzu talakawan arewa na cikin halin lahaula, sai Allah ya kyauta ya kawo mana dauki.”
Gamayyar Kungiyoyin Matsan Arewa da ke Kudancin Nijeriya ta dai bayyana cewa wannan sako ne ga dukkan matasan arewacin Nijeriya baki daya.