Hukumar Zabe mai zaman kanta reshe Jihar Zamfara, ta shirya taron wayar da kai kan ga nakasassu da (PWDs), jami’an zabe (EOs). A Dakin Taron Hukumar dake Gusau. Da yake jawabi a lokacinTaron , kwamishinan zabe mai zama Dakta Mahmud Isa ya cewa sun shirya wannan Taron ne dan karfafa wa nakasassu gwiwa ne su bayyana abubuwan da suka fuskanta, da gano kalubalen da ake fuskanta, da kuma bayar da shawarwari masu ma’ana da za su taimaka wa Hukumar inganta samun damar zabe da shiga a fadin Kananan Hukumomi 14 na Jihar Zamfara.
Dakta Mahmud Isa ya ce manufar shirin shine karfafa fahimtar kalubalen da nakasassu ke fuskanta yayin ayyukan zabe da kuma gano matakan da za a dauka don tabbatar da cewa za su iya shiga yadda ya kamata cikin tsarin dimokuradiyya.
Ya ce yayin da ake shirye-shiryen Babban Zaben 2027, INEC dole ne ta ci gaba da inganta ayyukan zabe na hada kowa da kowa, da samar da bayanai masu saukin isa, da kyakkyawar mu’amala, da kuma taimako ga masu zaben da ke bukatarsa. Haka kuma da yake jawabi wakilin hedikwatar Hukumar ta kasa Malam Musa Zubair ya ce Wannan shiri an shirya shi ne don karfafa fahimtar juna kan hada nakasassu, samun dama da kuma hanyoyin da Hukumar ta samar don inganta hakkin zaben Nakasassu (PWDs).
Ya ce shigar nakasassu a matsayin masu zabe, ‘yan takara da ma’aikatan zabe na da matukar muhimmanci ga dimokuradiyya. Saboda haka Hukumar ta ci gaba da jajircewa wajen gano da magance shingen da ke fuskanta a duk tsawon zagayowar zabe.














