| A |
ssalamu alaikum mabiyanmu masu albarka, kamar yadda muka saba duk mako mukan tsakuro wani batu na yabo da fifikon Annabi Muhammad SAW a kan sauran Annabawa da ma duk halittar Ubangiji baki daya, yau shafin na mu, zai yi tsokaci ne kan yadda Ubangiji tabaraka wata’ala, ya tsarkake iyalan Annabi SAW (Ahlul baiti) daga kazanta da aikata kowane irin sabo.
Annabi Ibrahim AS ya roki Ubangiji ya nesanta zuri’arsa daga bautar gunki wanda ake bautama wa, abun nufi wanda ake yanka jini ana bautar sa da nufin Ubangiji amma irin wanda yake fadar Annabi Sulaiman na sojoji ko ‘yan mazan jiya wannan ba gunki ba ne. Ya tabbata a Alkur’ani, mutanen Annabi Sulaiman suna kera masa gumaka na sojoji da tsoffin sarakuna ko kuma ‘yan mazan jiya, babu wanda ke zuwa gabansu da sunan bauta sai dai jinjina. Da wannan Malamai suke cewa, iyayen Annabi SAW suna kan addinin Annabi Ibrahim (Hanafiyya) kuma ya rokar wa zuri’arsa Ubangiji ya kare su daga bautar gunki kuma an amsa masa.
Amma ‘ya’yan gidan Manzon Allah SAW na cikin bargon nan (Annabi SAW, Sayyadina Ali, Sayyada Fatima, Hassan da Hussaini), ba wasu: A’li Akil, A’li Ja’afar, A’li Abbas ba; Allah ya kawar musu da kazanta (Giya, Caca, Bautar gunki, da Rantsuwa da kemaren tsafi), don haka, ‘ya’yan gidansa mai tsarki na cikin bargo komai za a yi, ba za su iya yin sabo ba. Tarihin Sayyadina Ali ya tabbatar da haka, duk yadda makiya suka yi don su tilasta shi ya yi sabo sai dai su gaji su bar shi, a karshe su ce “Allah ya yi gaskiya” suna nufin wannan Ayar. Haka Sayyada Fatima da ‘ya’yanta, ba za su iya yin sabo ba.
A nan, za mu kara gane banbancin Annabi SAW da Annabi Ibrahim AS ba kusa suke ba. Ya roki daya an ba shi amma Annabi SAW, Allah bai fadi inda ya roka ba amma sai da aka ba shi abinda Annabi Ibrahim AS ya roka kuma aka hado shi da gara.
Annabi Ibrahim AS, da mutanensa suka kama shi za su sanya shi a wuta, wuridin da yake yi, shi ne “Hasbiyallah…” sai Allah ya sanya wutar ta zama lambu (aminci a gare shi), amma Annabi SAW, Ubangiji ne ya ce masa, “ya kai wannan Annabi, Allah ya isar maka – Ya Ayyuhan nabiyyu hasbukallah…”
A nan, za mu gane cewa, Annabi Ibrahim AS, shi ya yi wuridi amma Annabi SAW, Ubangiji ne ya yi masa wuridi da kansa.
Annabi Ibrahim AS, ya yi Hijira zuwa garin da ake bautar Ubangiji, misali mu ce, daga Yamen zuwa Falasdinu inda Kur’ani ya ke cewa, “Inni Muhajirun ila rabbi sayahdin – ni na yi hijra zuwa ga Ubangiji na, zai shiryar da ni.” Amma Annabi SAW tafiyar da shi aka yi. Da fadinsa “Subhanallazi asra bi abdihi… – tsarki ya tabbata ga wanda ya tafiyar da bawansa …”
A nan, za mu gane cewa, Annabi Ibrahim AS, shi yake tuka kansa, amma Annabi SAW, shi Ubangiji ne ya tuka shi.
A wani wuri kuma da Ubangiji ya tattaro duka Manzonninsa, da fadinsa “Tilkarrusulu faddalna ba’dahum ala ba’ad – wadan can Annabawan, mun fifita wasu akan wasu”. Amma “Warafa’a ba’dahum darajat – wasu mun daga darajarsu akan wasu”.
A nan, za mu iya fahimtar cewa, duk Ubangiji ya fifita Manzonninsa akan wasu, amma ya nuna cewa ya daga darajar Annabi SAW a kan dukkansu.
In mun dauka kirarin da Ubangiji ya yi wa Annabi Musa AS da fadinsa “wakallamallahu Musa taklima – Ubangiji ya yi maganganu da Annabi Musa”, Annabi Musa shi yake zuwa da kansa inda Ubangiji ke ganawa da shi amma Annabi SAW, inda aka gana da shi, a saman sama, (Dana Fatadalla, fakana kaba kausaini au adna, fa’auha ila abdihi ma’auha), a lokacin an riga an shige Jibrilu, sannan duk aka yi wannan tafiyoyi – Dana Fatadalla, har ya zama kamar kausani ko kuma mafi kusa da haka ma. Wadanda ke fassarawa da cewa, (fa’auha ila abdihi ma’auha), Mala’ika Jibrilu ne ya yi wa bawansa Annabi Muhammad SAW wahayi, lallai kafarsu ta zame, ya dace a yi gyara. Da yawa a Tafsiri, Shehu Ibrahim Inyass Kaulaha zai ce, Mai tafsiri Jalal Arabi ya ce anan, amma fa kafarsa ta zame, ba haka abun yake ba!
A nan gabar ne, Shehu Ibrahim Inyass ke sharhi da cewa, “fa’auha ila abdihi ma’auha”, kalmar “ma” itace a ayar (wayakluku “ma” la ta’alamun), da ita ake halartar komai.
A nan, za mu gane cewa, Ubangiji ya yi magana da Annabi Musa ta shamaki amma da zai yi magana da Annabi SAW, gaba-da-gaba aka yi. Ubangiji ya fada mana cewa, Annabi Musa AS ya nemi ya ga Ubangiji amma bai amsa masa ba, amma ya gaya mana cewa, (ma kazabal fu’adu ma ra’a – zuciyar Annabi SAW ba ta karyata abinda idonta ya gani ba), kuma ya ruwaito mana abinda ya faru da Annabi Musa AS lokacin da aka tambaye shi, (Menene a hannunka ya Annabi Musa?) Duk abinda ya faru tsakanin Ubangiji da Annabi Musa AS, sai da Ubangiji ya ba mu labarin komai amma a yayin zantawarsa da Annabi SAW, sai dai kawai aka ji ya ce, (fa auha ila abdihi ma’auha – sai ya yi wahayi ga bawansa) babu wani cikin halitta da ya isa yasan me aka yi masa wahayi! Don a samu saukin wannan ayar, wasu malamai suka ce, Ubangiji ya yi wa bawansa wahayin komai, ma’ana ya sanar da shi komai.
Yana daga cikin abinda Fakrurrazi ya bayyana a Tafsirin ayar (Tilkarrusulu…), duka al’ummar Musulmi sun hadu cewa, ubangiji ya daga darajar wasu Annabawa akan wasu, wani Annabi yafi wani Annabi, amma Annabi SAW in aka hade dukkansu, ya fi su, in aka yi gogayya daya bayan daya, ya fi kowa, saboda irin aikinsa ba kamar na su ba.
Za mu iya gane hakan ta fuskoki kamar haka:
1 – An aiko Annabi SAW don ya zama rahama ga duk halitta (wama arsalnaka, illa rahmatan lil alamin) amma kowanne Annabi, rahama ne ga duk iya kauyensa (mutanensa), iya kacin wadanda suka yi imani da shi, sauran kuwa, sai ya ce duk a jefa su a wuta. Uwa uba Shari’ar Annabi Musa, me cewa, idan kun hadu da Larabawa ko Farisawa, ku kira su zuwa ga Addininku, idan sun bi, su zama bayinku, idan sun ki, ku kashe su gaba daya (Mata da Maza, yara) kuma sun ce wai Allah ne ya fadi haka. Ubangiji ba zai fadi haka ba. Don haka, suke kashe Falasdinawa, domin su a wurinsu ibada suke yi.
Don haka, fifikon Annabi SAW akan sauran Annabawa a fili yake. An aiko shi ga duk duniya, su kuma ga mutanen kauyensu kawai. Kuma shi yasa, Annabi SAW ya zama mafi rahamar halitta, don ba za a samu wani a saman shi ba. Tunda ya zama rahama ga duk halitta, to ya zama shugaban halitta.
Annabi SAW ya ce, hannun da ya bayar, ya fi hannun da ya amsa.
… Za mu ci gaba daga (2) a mako mai zuwa.
Alhamdulillah… irin wannan karatu da zai nuna maka daraja da soyayya ta Annabi SAW, shi al’ummar Annabi SAW ke bukata ba wanda zai koya maka cin fuska ga reshi da iyalan gidansa ba.














