Garin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ya karbi bakuncin daruruwan wakilai a babban taron jam’iyyar PDP mai cike da cece-kuce, inda dubban ‘yan jam’iyya da gwamnonin hudu suka taru a filin wasa na Lekan Salami, Adamasingba.
Wannan taron na tsawon kwanaki biyu daga ranar Asabar, 15 ga Nuwamba har zuwa safiyar Lahadi, 16 ga Nuwamba, 2025, an dai gudanar da abubawa masu yawa da suka hada da raye-raye da kade-kade tare da lika hotunan ‘ya’yan jam’iyya wadanda ke neman mukamai daban-daban a cikin filin wasan.
- Allah Ya Tsarkake Iyalan Annabi (SAW) Daga Kazanta
- Gwamnan Neja Ya Yi Allah-Wadai Da Sace Ɗaliban St. Mary A Papiri
Domin tabbatar da cewa an gudanar da taron ba tare da matsala ba, jami’an tsaron ‘yansanda da jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da rundunar Amotekun ta Jihar Oyo sun tsare manyan wurare a kusa da filin wasa, yayin da jami’an kula da zirga-zirga ke aiki ba dare ba rana don sarrafa yawan motoci a kan Titin Obafemi Awolowo da titunan kusa da shi.
Alamar farko na rashin jituwa a taron dai shi ne, yadda fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar suka dunga yage hotunan gwamnonin PDP guda biyu, Ademola Adeleke na Jihar Osun da Agbu Kefas na Jihar Taraba wadanda ba su halarci taron ba.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Ahmadu Fintiri (Adamawa); Caleb Muftwang (Filato); Bala Mohammed (Bauchi); Dauda Lawal (Zamfara) da kuma mai masaukin baki, Seyi Makinde na Jihar Oyo.
Taron kuma ya jawo shahararrun ‘yan PDP kamar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Adolphus Wabara da Cif Olabode George da tsofaffin gwamnoni irinsu Udom Emmanuelda Babangida Aliyu da Ibrahim Shekarau, da sauran manyan ‘yan jam’iyyar.
Shugaban kwamitin shirya taron kuma Gwamnan Jihar Adamawa, Umaru Fintiri, yayin da yake jawabi a taron, ya ce ‘yan Nijeriya za su sake kallon PDP don ceto kasa.
A cewarsa, “Ikon jam’iyya na nufin jam’iyya da aka gina sosai bisa ka’idojin karfin zuciya da kiraye-kiraye na dimokuradiyya domin ceto Nijeriya. Kuma a kowane lokaci bai kamata ta sauka daga layin da ka kafa ta ba.
“Nijeriya da ‘yan Nijeriya har yanzu suna kallonmu a matsayin wadanda suka taka rawa da ya dace da tsarin jam’iyyarmu. Hakika, Nijeriya ta koma baya tun lokacin da APC ta amshi mulki. Dole ne mu yarda cewa duk munanan abubuwan da suka faru a Nijeriya a cikin ‘yan shekarun nan sun shafi jam’iyyarmu. Ruhin jam’iyya har yanzu bai lalace ba saboda akwai maza da mata da suka yi imani da ginshikan jam’iyya.”
A nasa jawabin, Gwamna Makinde ya bayyana cewa babban taron Ibadan na 2025 za a dunga tunawa da shi a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci ga jam’iyya.
Ya ce, “Ina so in yi garsuwar maraba da kowa zuwa wannan taro, musamman mambobin PDP masu juriya. Bari in yi amfani da wannan dama don yin maraba da ku zuwa Ibadan, Jihar Oyo. Mun yi dogon gwagwarmaya don isa wannan matakin, amma ga mu a nan. Kuma da ni’imar Allah, wannan taro zai kasance taron da ya kawo juyin-juya hali ga PDP a kasa baki daya.”
Yayin da yake magana a madadin kungiyar gwamnonin PDP, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada hadin kan gwamnonin jam’iyyar. Ya ce, “Kamar yadda kuke gani, muna nan a yau a matsayin kungiya ta hadin kai don ci gaban wannan jam’iyya. Muna rokon kowa da kowa da ke nan da ya ba mu cikakken goyon baya domin mu ceci makomar Nijeriya. Ina fatan wannan babban taron ya yi nasara.”
A cikin sakon fatan alheri, shugaban kwamitin amintattu PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya bayyana taron a matsayin babban nasara ga jam’iyyar. A cewarsa, jam’iyyar ba za ta shude ba saboda taron ya kasance shaida ga juriyar mambobinta, ruhin dimokuradiyya da hadin gwiwar da mambobi ke da shi wajen bin ka’idodi da ci gaban Nijeriya, yana karfafa mambobin kwamitin gudanarwa su kasance masu rungumar shugabanci na gari don samun hadin kai.
Daya daga cikin muhimmancin sakamakon taron shi ne, korar wasu manyan mambobi saboda zargin ayyukan da suka saba wa jam’iyya. Wadanda aka kora sun hada da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike da sakataren jam’iyyar, Samuel Anyanwu da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose da mashawarcin shari’a na jam’iyya, Adeyemi Ajibade (SAN) da Umar Bature da AbdulRahman Mohammed da Mao Ohuambuwa da George Turner da Austin Nwachukwu da Abraham Ammah da kuma Dan Orbih.
Babban abin da taron ya kunsa shi ne zaben babban lauya daga Jihar Kebb, Kabiru Turaki a matsayin sabon shugaban jam’iyyar PDP. Sakatare taron, Sanata Ben Obi ya bayyana cewa Turaki ya samu kuri’u 1,516, wanda ya ba shi damar zama sabon shugaban PDP.
Haka kuma an zabi Mista Solarin Adekunle, a matsayin mataimakin sakataren tsare-tsaren al’amura na jam’iyyar, yayin da wasu ‘yan takara da dama suka sami dawowa mukamansu ba tare da hamayyar ba bayan janye ‘yan adawarsu.
A cikin jawabinsa na karbar mukami, Turaki ya ce ya fahimci girman nauyin da aka dora a wuyansa da na jagorantar kwamitin gudanarwa na jam’iyyar, yana mai kara cewa wajibi ne su cika aikin da aka dora musu ga ‘yan Nijeriya cikin aminci.
Ya bayyana cewa sabuwar shugabanci za ta fitar da ka’idojinta da tsarin aiki nan ba da jimawa ba, tare da jaddada cewa kwamitin zai fara aiki nan take. Yayin da yake jaddada cewa PDP ce kadai jam’iyyar siyasa a kasar da ta kiyaye asalinta tun farkon kafuwarta.
Ya ce, “Nauyin da kuka dora mana yana nufin cewa kuna kallo mu don mu kai ga ciki ga mutanen Nijeriya, kuma za mu yi haka. Ba mu yin tunanin karya cewa aikin da aka ba mu abu ne mai sauki. Jam’iyyarmu na cikin wani yanayi mai wahala yanzu, amma muna da karfin yin aikin da kuma karfin fuskantar kalubale.
“Ba da dadewa ba, za mu bayyana mene ne ka’idodinmu masu jagoranci da kuma yadda za mu cimma su. Lokacin da muke yin hakan, za mu fara aiki cikin sauri tun daga ranar farko. Yau, yayin da nake magana da ku, jam’iyyar siyasa daya tilo da ta ci gaba da rike sunanta ita ce jam’iyyar PDP. Wannan ya yiwu ne saboda wannan jam’iyya ce ta mutanen Nijeriya.”
Abin da ba a yi shakka a kai ba shi ne, babban taron ya gudana ne bisa saba wa hukuncin kotu da suka yi kokarin dakatar da shi, yayin da wakilai da masu jawabi daban-daban suka koma kan batun shari’o’in. Duk da haka, ga masu lura da siyasa, lokaci ne kawai zai nuna ko sakamakon zai taimaka wajen kawo karshen rikice-rikicen da ke damun jam’iyyar ko kuwa zai kara haddasa su.














