Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a janye dukkan ƴansandan da ke gadin manyan mutane (VIPs) a fadin ƙasar nan, domin mayar da su ga aikinsu na asali na kare al’umma. Wannan sabon umarni ya fito ne bayan wani taron tsaro da shugaban ƙasar ya gudanar a Abuja tare da shugabannin Sojoji, da rundunar DSS.
A cewar umarnin fadar shugaban ƙasa, daga yanzu duk wani babban mutum da ke buƙatar kariya zai nemi jami’an tsaro daga Hukumar NSCDC maimakon ƴansanda. Wannan mataki ya biyo bayan ƙarancin ƴansanda a sassa da dama na ƙasar, musamman yankunan da ke da nisa, lamarin da ya sa ba a samun wadatacciyar kariya ga jama’a.
- Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari
- ’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi
Shugaba Tinubu na da burin ƙara yawan jami’an ƴansanda a ƙananan hukumomi da ƙauyuka, domin inganta tsaro a lokacin da ake ci gaba da fama da ƙalubalen tsaro iri-iri. Tuni shugaban ya amince da ɗaukar sabbin ƴansanda 30,000, tare da haɗa kai da jihohi wajen inganta cibiyoyin horaswa na rundunar a fadin ƙasa.
Taron tsaron na ranar Lahadi ya samu halartar manyan jami’an tsaro, ciki har da Babban Hafsan Sojan Ƙasa, da Laftanar Janar Waidi Shaibu; da Babban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke; da Babban Sufeton Ƴansanda, Kayode Egbetokun; da Daraktan DSS, Tosin Adeola Ajayi.














