Jam’iyyar APC a Jiharr Katsina ta umarci mambobinta su tabbatar da samun nasarar rangadin da Gwamna Dikko Raɗɗa ke gudanarwa a faɗin jihar.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Sani Aliyu Daura ya bayar da wannan umarni bayan wani taron kwamitin zartaswar jam’iyyar da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar.
- Gwamnatin Katsina Da UNICEF Za Su Yi Wa Yara Miliyan 2.8 Allurar rigakafi A Katsina
- Tarihin Alhaji Isa Kaita Wazirin Katsina (3)
Ya ce ziyara zuwa yankunan ƙananan hukumomi 34 a jihar na da nufin duba ayyukan da ƙananan hukumomi suka aiwatar ba don gangamin siyasa ba.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar ya gargaɗi mambobin jam’iyyar masu neman muƙamai daban-daban su guji ɗaukar nauyin magoya bayansu wajen ɗauka ko nuna fastoci a lokacin rangadin.
Sai dai, Alhaji Sani ya yi cikakken bayani kan shirin rajistar ƴan jam’iyyar, yana mai cewa jami’ai guda 2 za su gudanar da rajistar a kowacce mazaɓa.
Ya buƙaci ‘ya’yan jam’iyyar su mallaki lambar katin shaidar ɗan ƙasa ta NIN wadda ita aka fi buƙata wajen yin rajistar a zamanance.
Ya bayyana cewa jam’iyyar na buƙatar yi wa sama da mambobi miliyan 3 rajista sama da mambobin miliyan 1.5 da aka yi wa rajista a lokacin shirin da ya gabata.
Shi ma da yake jawabi, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Bala Abu Musawa ya yi ƙarin haske kan rangadin na gwamna da kuma rajistar mambobin jam’iyyar na zamani.
Alhaji Bala Abu Musawa ya bayyana farin cikin cikinsa bisa ɗimbin magoya bayan jam’iyyar da suka taru a ƙaramar hukumar Faskari, sai dai ya yi gargaɗin cewa jam’iyyar ba za ta lamunci rashin biyayya ba.
Ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar a jihar su nuna dattako a lokacin ziyarar aiki ta gwamnan zuwa majalisun ƙananan hukumomi 34 na jihar.
A dukkan ƙananan hukumomin, gwamnan ya gana da manyan masu ruwa da tsaki ciki har da sarakunan gargajiya da na addini da ƴan siyasa da matasa da ƙungiyoyin mata.
A ziyararsa zuwa Malumfashi, Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon kayan tallafi domin ƙarfafa harkokin kasuwanci ga al’umma tare da raba motoci ga jami’an ƙaramar hukumar da jagororin jam’iyyar APC.
Haka zalika a Ƙafur, gwamnan ya ƙaddamar da tallafin jari ga ƴan kasuwa ƙanana dubu ɗaya da ɗari takwas da hamsin da tara, sannan ya bayar da naira dubu talatin-talatin ga wasu mutane dubu ɗaya domin tallafa musa wajen bunƙasa sana’o’insu.














