Kotun Tarayya da ke Kaduna ta yanke hukunci kan cewa Hukumar EFCC ta keta ƴancin Rabiu Auwalu Tijjani, wani fitaccen ɗan kasuwa daga Kano, lokacin da ta wallafa sunansa da hotonsa a matsayin wanda ake nema ba tare da umarnin kotu ba. Mai shari’a H. Buhari ta bayyana matakin hukumar a matsayin abin da bai yi daidai da kundin tsarin mulki ba, kana kuma ya wuce iyakar ikon ta.
Tijjani ya shigar da ƙara bayan EFCC ta bayyana shi a matsayin wanda ake nema a ranar 11 ga Yuli 2025, kan rikicin kasuwanci da ya taso tsakanin shi da wani dan kasuwa Ifeanyi Ezeokoli a cinikin zinari na 2022.
- EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra Chris Ngige A Abuja
- Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Garkuwa Da Kashe Mai Gidansa A Kano
Bayanan kotu sun nuna cewa ɓangarorin biyu sun amince da biyan ₦26m wanda aka biya fiye da kima, sai dai binciken lissafi mai zaman kansa ya gano ƙarin matsala ta sama da dala miliyan biyu a gefen Tijjani. Lamarin da tuni ya isa hannun DSS domin bincike, amma daga baya Ezeokoli ya kai ƙara EFCC, wadda ta fara tuntubar Tijjani ta WhatsApp. Duk da haka, kotu ta ce hukumar ba ta sake gayyatarsa ba kafin ta wallafa shi a matsayin wanda ake nema, abin da ya shafi mutuncinda da harkokinsa na kasuwanci.
Mai shari’ar ta jaddada cewa EFCC na da ikon bayyana duk wani wanda ake nema, amma wajibi ne ta bi matakin doka, ciki har da neman izini daga kotu. Ta kuma ce samun damar kama mutum daga kotun majistare ba ya nufin hukumar na iya wallafa shi a bayyanar jama’a. Kotun ta soki hukumar saboda shiga cikin rikicin kasuwanci wanda ya kamata a warware shi ta hanyoyi na lumana, musamman ma la’akari da cewa DSS na gudanar da bincike a kai.
Kotun ta ayyana wallafar EFCC a matsayin tauye ƴanci, da keta ƙa’idojin riyaya da kuma tauye bin diddigin doka. Saboda haka ta umurci hukumar ta cire hoton da ta wallafa, ta bai wa Tijjani haƙuri a bainar jama’a, sannan ta biya shi N₦5m a matsayin diyya.














