ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Waiwaye Adon Tafiya: Manyan Nasarorin Da Aka Cimma A Dangantakar Kasashen Afirka Da Sin A 2025

by Sulaiman
1 week ago
Afirka

Kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen Afirka da Sin kamar rana ce da ta kwallaro, babu wanda zai ce bai ganta ba sai makaho, ko shi ma makahon sai ya ji zafinta.

A shekarar 2025, hadin gwiwar Sin da Afirka ta sake samun muhimmin ci gaba ta hanyar ziyarar aiki ta diflomasiyya mai zurfi, zuba jari a manyan kayayyakin more rayuwa, da kuma hada hannu ta bangarori daban-daban kamar kimiyya da fasaha wanda hakan ke nuna ci gaba a daidaiton manufofi tsakanin bangarorin biyu.

Bari mu kawo wani dan takaitaccen bayani game da manyan ci gaba da aka cimma a hadin gwiwar Sin da Afirka a shekarar 2025, tare da warware zare da abawa kan abin da sabon ci gaban ke nunawa dangane da hadin gwiwar kasashen a nan gaba.

ADVERTISEMENT

 

Ziyarar aiki da ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya kawo Afirka

LABARAI MASU NASABA

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?

Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing

A ci gaba da al’adar fiye da shekaru 30, Ministan Harkokin Wajen Sin Wang Yi ya ziyarci kasashen Afirka da dama a tsakanin 5-11 ga watan Janairun 2025 don sake tabbatar da dangantakar diflomasiyya da kuma binciko sabbin hanyoyin hadin gwiwa. Wannan ziyarar ta sake tabbatar da manufar ci gaba da cin moriyar juna a tsakanin bangarorin biyu.

 

Baje kolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afirka na hudu a Changsha

An gudanar da wannan taron baje kolin na hudu daga 12 zuwa 15 ga watan Yunin bana a Changsha, babban birnin lardin Hunan. Baje kolin ya tattaro kusan kamfanonin Sin da Afirka 4,700, kuma an baje kolin kayayyakin Afirka sama da 800 daga kasashe da dama.

An gudanar da taron ne tare da bikin cika shekaru 25 na taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), wanda hakan ke jaddada tsarin ci gaba na dogon lokaci na ci gaba da huldar Sin da Afirka.

 

Fadada ciniki da katse shingen haraji zuwa sifili ga kasashen Afirka

A shekarar 2025, cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka ta ci gaba da bunkasa sosai, cinikayyar Sin da Afirka a cikin watanni biyar na farko bayan katse shingen haraji ta karu da kashi 12.4% a shekara. Sin ta dakatar da haraji kashi 100 bisa 100 ga dukkan kasashen Afirka 53 wadanda suke da huldar diflomasiyya da kasar. Wannan manufar ta rage shingen ciniki sosai kuma ta inganta damar shiga kasuwa da fitar da kayayyaki daga Afirka. Wannan fadada manufofin ciniki ya nuna yadda aka sauya tsarin yarjejeniyar cinikayya daga yarjejeniya ta dan wani lokaci daya ko mai iyaka zuwa hadewar kasuwa mafi tsari kuma ta dogon lokaci.

 

Mu’amalar jama’a, al’adu, ilimi da bude ido

Tattaunawar Jama’a da Jama’a ta Afirka da Sin wacce ta gudana a watan Mayu na 2025 a Lusaka, Zambia, ta tattaro kungiyoyin jama’a, shugabannin kasuwanci, ‘yan kasuwa, da masu tsara manufofi daga Afirka da Sin. Ta jaddada hadin gwiwa tsakanin al’ummar bangarorin biyu fiye da yadda bangare daya kacal ke mu’amalarsa.

A irin wannan tattaunawar ta hadin gwiwa da ta gudana a wani taron hadin gwiwa na 2025 a birnin Jinhua na lardin Zhejiang, an sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi 33, wadanda suka shafi ciniki, saka hannun jari na kasashen waje, kwangilar injiniyanci, gina rumbunan ajiya a kasashen waje, wadanda darajarsu ta kai yuan biliyan 40.11 (kimanin dalar Amurka biliyan 5.63).

Bayan kasuwanci, taron Jinhua ya hada da musayar al’adu da yawon bude ido, inda aka gudanar da bikin baje kolin al’adu da yawon bude ido na Afirka na farko.

 

Hadin gwiwar kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire da hukumar tarayyar Afirka

A watan Satumba na 2025, Hukumar Tarayyar Afirka (AUC) da Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha ta Sin sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna don zurfafa hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha. Daga 19-21 ga watan Nuwamban 2025 kuma, an gudanar da taron hadin gwiwa kan ci gaban kirkire-kirkire na Sin da Afrika a birnin Wuhan, da nufin daidaita hadin gwiwar kimiyya da fasaha kan bukatun ci gaban Afirka, ciki har da makamashi mara cutar da muhalli (green energy), biranen kimiyya, ci gaba mai dorewa, da sauransu.

 

Hadin gwiwar fasaha a ɓangaren kula da muhalli

Cibiyar Hadaka ta Sin da Afirka mai Amfani da Tauraron Dan Adam (CACSA), ta fadada hadin gwiwarta da Afirka a shekarar 2025. Tun kafuwarta a shekarar 2023, ta rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi da kasashen Afirka 16, inda ta kafa na’urori 14 na kula da sararin samaniya masu amfani da tauraron dan adam wadanda ke tallafawa sama da hotuna 70,000 masu inganci daga hangen nesa. Wannan yana tallafawa tsare-tsaren birane, sa ido kan yadda ake amfani da kasa, kula da tekuna ko koguna, sa ido kan muhalli, da sauransu.

Ta hanyar shirye-shirye a fannin kimiyya, samar da makamashi mara cutarwa ga muhalli, da kayayyakin more rayuwa na dijital, Sin da Afirka suna zurfafa hadin gwiwa ba wai kawai a fannin kayayyakin more rayuwa da aka fi sani kamar hanyoyi, layin dogo, tashoshin jiragen ruwa ba, har ma a fannoni masu muhimmanci na “zamani” da karni na 21 ke bukata don ci gaba.

 

Masu karatu, mu tambayi kanmu mana, me wannan gagaruman sabbin nasararorin hadin gwiwar Afirka da Sin ke nufi a nan gaba?

Daga cinikayya, da samar da ababen more rayuwa zuwa hadin gwiwa na dabarun fasaha da zamantakewa ta zamani da suka hada da kimiyya da fasaha, tattalin arzikin dijital, samar da makamashi mara cutarwa ga muhalli, da kirkire-kirkire. Hakan yana nuna ci gaba daga hadin gwiwa mai karfi irin na baya zuwa ga hadin gwiwa mai fadi a bangarori daban-daban na zamani, masu amfanarwa ga juna. Yarjejeniyar Kimiyya da kirkire-kirkire ta 2025 tare da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da hadin gwiwar CACSA shaida ne na wannan ci gaban sauyin.

Idan aka aiwatar da wadannan yarjejeniyoyin hadin gwiwar yadda ya kamata, wannan hadin gwiwa mai zurfi zai iya taimakawa Afirka wajen hanzarta gyara da ci gaban masana’antunta da komawa cikin zamani. Har ila yau, hakan zai sanya Sin da Afirka a matsayin abokan tarayya wajen tsara sabon tsarin ci gaban duniya mai bangarori daban-daban.

 

 

 

 

 

 

 

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?
Ra'ayi Riga

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?

December 17, 2025
Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing

December 16, 2025
Waiwaye Adon Tafiya : Tasirin Sin A Kan Afirka Ta Fannin Fasahar AI
Ra'ayi Riga

Waiwaye Adon Tafiya : Tasirin Sin A Kan Afirka Ta Fannin Fasahar AI

December 15, 2025
Next Post
Me Ya Sa Ya Kamata Kasashen Afirka Su Bunkasa Tattalin Arziki Tare Da Kare Muhalli?

Me Ya Sa Ya Kamata Kasashen Afirka Su Bunkasa Tattalin Arziki Tare Da Kare Muhalli?

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.