A bisa wani sabon binceke da wasu masana a fannin noman alkama a kasar nan suna gudanar sun bayyana babban dalilin da ya janyo aka samu raguwar noman amfanin a kasar nan.
Nijeriya dai, ta kasance a baya ta na noma alkamar mai yawa, musamman ganin cewa, kasar na da kasar yin noma mai inganci.
- CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Murnar Tsakiyar Yanayin Kaka Ta Yin Amfani Da AlAdun Haduwar Iyalai
- Da Dumi-Dumi: Sarauniyar Ingila, Elizabeth Ta Rasu
A wani hasashe da aka yi a kan fannin na noman Albarsar a kasar nan, nomanta ya ragu daga tan dubu 600 da ake nomawa a kasar, inda a yanzu, ake noma tan 400.
Sun yi nuni da cewa, a yayin da a yanzu a fadin duniya aka samu karancin Alkamar, musamman yadda yakin da ake yi a kasar Ukraine ya jano karancin a duniya, da ace gwamnatin kasar ta mayar da hankali wajen nomanta, musamman ta hanyar samarwa da manoma a fannin tallafin da ya kamata, da yanzu Nijeriya ta daga tuta wajen kara samun masu zuwa sayen ta daga wasu kasashen waje, inda kuma hakan, zai kara bunkasa samar da kudaden musaya na kasar waje ga gwamnatin kasar.
A cewarsu, kamata ya yi ace, lokacin da aka bullo da shirin aikin noma a kasar nan na Anchor Borrowers da ke a karkashin kulawar Babban Bankin Nijeriya, da gwamnatin ta mayar da hankaili wajen san ya fannin noman na Alakamar da an kara wada samar da wadatacciyar a kasar, har da wacce za iya fitarwa zuwa waje don sayarwa.
Sun buga misali da yadda a lokacin da gwamnatin tarayya mai ci ta karbi madafun iko na kasar, ta fi mayar da hankali waken samar da shirye-shieye da tsare-tsaren da za su habaka noman Shinkafa ‘yar gida.
Sun yi nuni da cewa, ganin yadda ake kara samun bukatar Alkamar a kasar nan, inda a yanzu ana samar tan miliyan 4.2.
A bana akwai manoma dubu 9 zuwa dubu 10 da suka samu tallafin shirin duk da wasu kananan manoma sun mai da hankali wajen noman shinkafa ko masara.
Hakan zai bunkasa abin da ake nomawa, idan har ana iya aiwatar da hakan Nijeriya za ta iya yin kafada da sauran kasashen waje.
Har ila yau, masanan sun janyyo wasu daga cikin kalubalen da suka haifar da raguwar nomanta a kasar nan, inda suka bayyana cewa, rashin mayar da hankali a fannin nomanta da gwamantin tarayya ba ta yin a daya daga cikin abin da ya aka samu raguwar nomanta a kasar.
A cewarsu, wasu daga cikin kalubalen sun hada da, rashin samun ingantaccen irin alkama, inda suka bayyana cewa, a yanzu akasarin irin na Alkamar da wadansu manoma ke amfani da shi ba ya samun gibi mai yawa.
Sai dai, sun danganata hakan a kan karancin kan rashin fitar da kudade don cibiyoyin bincike a kaar su samu damar gudanar da kyakyawan binciken akan irin da ke da inganci.
Har ila yau, akwai kuma kalubale na rashin yadda farashinta yake a wasu kasuanni tare da kuma karancin kayan sarrafa ta wasu kamfanoni a kasar ke sarrafata, inda hakan ya kara zanyo kasar nan ta dogara wajen shigo da ita daga kasashen waje da ke nomanta da yawa.
Har ila yau, masanna sun yi nuni da cewa, rashin samar da tallafi ga manomanta a kasar nan, musamman ga kananan manoma, hakan na kara durkusar da fannin a kasar nan.