A halin da ake ciki kuma, Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya zargi PDP da dan takarar shugaban kasanta, Atiku Abubakar waje satar amsa daga manufofin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Tinubu ya zargi Atiku da satar manufofin Buhari guda biyar wanda ya saka su a cikin shafukan yakin neman zabensa guda 74. Dan takarar shugaban kasa na APC ya ce jam’iyyar PDP ba ta da kwarewawajen yin sahihin adawa.
- Kasar Sin Mai Wadata Za Ta Kara Samar Da Damammaki Ga Duniya
- Neymar Ya Zura Kwallaye 200 A Kungiyoyi Uku
Babban mai magana da yawun dan takarar wanda shi ne daraktan hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zabe, Festus Keyamo (SAN), shi ya bayyana hakan lokacin da yake mayar da martani kan ikirarin daraktan yada labarai na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na PDP,
Dele Momodu kan fejina 80 da Tinubu ya bayyana a matsayin manufofinsa a Abuja ranar Asabar a filin wasa na MKO Abiola.
Da yake mayar da martanin, Keyamo wanda ya kasance tsohon ministan samar da ayyuka yi ya ce tawagar kamfen din Atiku marasa amfani ne.
Ya ce ya yi tsammanin cewa Momodu zai yi cikakken bayani a tsakanin kundin mai dauke da shafuka 93 da Tinubu ya kaddamar da filin wasa na MKO Abiola.
Ya ce Atiku ya sace manufofi guda biyar na Buhari wanda ya cike a kundin yakin neman zabensa.
Ya ce daga cikin manufofin akwai fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci da sake farfado da wutar lantarki wajen bunkasa tattalin arziki, wanda kamata ya yi ya kirkiri nasa sababbin manufofin ba wai ya tsaya satar na Shugaba Buhari ba.
Keyamo ya ci gaba da bayyana cewa Momodu bai da abun da zai iya sukar Tinubu, domin ya yi kokarin kawo nasa manufofin ba tare da ya sata dagawurin wani ba.
Zan Fallasa Badakalar APC – Atiku
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai fallasa dukkan badakalar da jam’iyyar APC ta yi lokacin da take rike da madafun iko bayan ya samu nasarar zama shugaban kasa.
Atiku ya bayyana haka ne lokacin da yake yi wa magoya bayansa jawabi a ranar Lahadin da ta gabata, ya siffanta babban zaben 2023 a matsayin raba gardama game da kwazon APC.
Ya kara da cewa jam’iyyar APC da kuma dan takarar shugaban kasarta, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu suna so su ci gaba da mulki duk da irin zagawa da suka yi, amma jam’iyyar PDP ba zata taba barin su ba.
Ya ce, “Lokacin da muka ziyarci Benin na bayyana manufofi na kararawajen gudunar da ayyuka da zai hade kanmu da ceto kasarmu Nijeriya.
“Shiri ne wanda ya kunshi dogon zango mai matukar kalubale a gare mu a halin yanzu, wanda dalilin da ya saya kin neman zabena ya karkata wajen tallafa su ga ‘yan Nijeriya kenan.
“A bangarena da kuma duk wanda yake a cikin jam’iyyar PDP, babban zaben 2023 shi ne zakaran gwajin dafi da zai auna kwazon APC.
“Jam’iyya mai mulki na kokarin gudu daga rashin gwazon su wanda hasali ma suna mayar da hankali akan abubuwan da ba su ta’allaka da zaben ba. Amma mu ba za mu taba basu dama ba. Sai mun bankado duk irin tsula tsiyar da suka tabka mun bayyanawa ‘yan Nijeriya.
“Ko da yake hakan ba zai gamsar ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, karmu sake maimaita kuskuren da muka yi a baya.
“Wannan ya sa muka hadu domin mu bayyana muku manufofin kowacce jam’iyyar siyasa domin yanke hukuncin da ya dace lokacin zabe.”
Atiku jaddada cewa a matsayinsa na dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, zai mayar da hankali ga dukkan matsaloli da suka addabi kasar nan.
Sulhu Tsakanin Atiku Da Wike Ya Sha Ruwa
Daga karshe dai, sulhu a tsakanin gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sha ruwa.
Wike ya bayyana cewa ba zai yi wa jam’iyyar PDP yakin neman zabe ba saboda ba a tuntube shi ba lokacin da aka dauki mambobin kamfen a cikin jiharsa.
Ya kara da cewa hotonan Atiku da na shugaban jam’iyyar PDP, Sanata Iyorchia Ayu sun yi batan dabo a cikin jiharsa saboda ba su san yayi yakin neman zabe a mataki na tarayya a jam’iyyar.
Wike ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da kwamitin kamfen din jam’iyyar PDP a Jihar Ribas wanda ya gudana a garin Fatakwal.
Ya ce dan takarar shugaban kasa a jam’iyyary a zabi makiya Jihar Ribas a cikin kwamitin yakin neman zabensa na 2023.
Gwamnan ya ce, “Wasu mutane suna tambaya na kan dalilan da suka sa ba a ganin hotunan dan takarar shugaban kasa da kuma na shugaban jam’iyyar. Na ce musu me ye suke magana a kai? Dan takarar shugaban kasa ya shiga jihata ya dauko mambobin kwamitin yakin neman zabensa ba tare da gudummuwar gwamnan jihar ba.
“Dan takarar shugaban kasa ya shiga Jihar Ribas ya dauko wadanda yake bukata ba tare da bayar da gudummuwar gwamna ba. Sun ce basa bukata na a yakin neman zabensu, kuma hakan na nuna cewa ba sabukatar mutanen Jihar Ribas ne a cikin kwamitin kamfen dinsu.”
Wike ya ce shi da sauran ‘ya’yan jam’iyyar a jihar za su yi kamfen ne kadai ga dan takarar gwamna da na sanata da sauran wasu mukamai, amma ban da na dan takarar shugaban kasa.
Ya ce, “Idan da suna bukatarmu a cikin yakin neman zabensu da sun tuntube mu. Idan yana tunanin muna da muhimmanci, to da ya zo wurinmu. Babu wanda ya isa ya jagoranci Jihar Ribas fiye da ni a matsayina na gwamnan jihar.”
Gwamnan ya kara da cewa kowacce karamar hukumar guda 23 da ke jihar tana da hanyoyin da take bi wajen hada mutanenta.