Gidan rediyon Premier da ke Jihar Kano, ya yi Allah wadai da cin zarafi da wani jami’in dan sanda ya yi wa ma’aikacinta a lokacin da ya ke daukar rahoto.
Dan jaridar mai suna Muhammad Bello Dabai, ya sha mari, duka da kuma zagi tare kuma da tursasawa daga gurin wani jami’in dan sanda a lokacin da ya ke kokarin daukar hoto domin hada labara.
- Buhari Ya Ba Ni Tabbacin Za A Gudanar Da Sahihin Zabe A 2023 – Atiku
- Na Ji Radadin Da Zafin Rasuwar Shehu Malami – Buhari
Manajan sashen labarai na gidan rediyon, Malam Mukhtar Yahaya Usman ya sanar da hakan ga manema labarai.
Yahaya, ya ce tun da farko lamarin ya faru ne bayan da wani mutum da ya ke fuskantar tuhuma a hannun jami’an ‘yansanda ya kubuce musu a lokacin da ake tafe da shi zuwa asibitin Abdullahi Wase da ke birnin Kano domin a duba lafiyarsa.
Sanarwar ta kara da cewa bayan da wanda ake tuhuma ya kubuce sai ya biyo ta gaban gidan rediyon, inda a nan ne mutane su ka cimma masa kafin daga bisani jami’an ‘yansanda su ka karaso su tafi da shi.
Hakazalika Mukhtar Yahaya ya ce bayan da jami’an ‘yansandan su ka kama wanda su ke tuhumar daga nan ne Muhammad Bello Dabai ya dauko waya domin daukar hoton abin da ya faru, wanda a nan ne wani jami’in dan sandan ya fara zagi tare da marin dan jaridar duk da cewa ya gabatar da kan sa tare da nuna katin shaidar aiki.
Bayan shan mari da duka jami’in dan sandan ya tursasa Muhammad Bello Dabai shiga cikin motarsu tare da kwantar da shi a kasan motar, inda su ka tafi da shi caji ofis su ka tsare shi na wani lokaci.
Ana dai yawan zargin jami’an tsaron kasar nan musamman ‘yansanda da keta hakkin ‘yan adam.
A baya–bayan nan sai da kungiyar kare hakkin bil Adama (Amnesty International), ta ce ana samun yawaitar kai wa ‘yan jaridar Nijeriya samame tare da tsorata su, abin da ya sa ‘yan jaridar ke aiki cikin yanayi na tsoro da firgici.