Allah ya yi wa tsohon shugaban Jami’ar Bayero ta Kano kuma tsohon shugaban Jami’ar Fasaha Ta Tarayya da ke Minna, Farfesa Ibrahim Umar rasuwa.
Iyalan mamacin ne suka tabbatar wa da Leadership Hausa rasuwar, inda suka ce Farfesan ya rasu ne a Kano ranar Litinin.
- Zan Tabbatar Da An Yi Sahihin Zaben Da Ba A Taba Irinsa Ba – Buhari
- Tinubu Ya Godewa Buhari Kan Amincewa Da Kara Wa’adin Kwanakin Daina Karbar Tsoffin Kudade
Marigayin, wanda shi ne dan Nijeriya na farko da ya fara koyar da Physics a BUK a shekarar 1976, ya zama mataimakin shugaban Jami’ar daga 1979 zuwa 1986.
A lokacinsa, sabon rukunin Jami’ar ya samu manyan ci gaban ababen more rayuwa, wanda ya hada da ginin gudanarwa na ilimi, dakunan kwanan dalibai, bunkasa ci gabn manyan ma’aikata da kuma hanyar sadarwa.
A shekarar 1978, ya yi aiki a Majalisar Tsarin Mulki ta Kasa wadda ta tsara kundin tsarin mulkin Jamhuriya ta biyu, kuma ya wakilci Nijeriya a Majalisar Zartarwa ta Majalisar Makamashi ta Duniya daga 1990.
Ya kuma kasance mamba na tawagar Nijeriya a babban taron Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (International Atomic Energy Agency) a 1989, kuma an nada shi Darakta-Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya a 1989.