Rundunar ‘yansandan Jihar Osun ta sanar da kama wani jami’in DSS na bogi da wasu mutane bakwai da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da wasu mutane uku bisa laifin fashi da makami.
Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Yemisi Opalola, ta shaida wa manema labarai ranar Talata a Osogbo cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wasu ayyuka da suka gudanar a jihar.
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Kai Zuciya Nesa Game Da Batun Kumbon Farar Hula Da Ta Harbo
- Masana’antun Kasar Sin Sun Taka Rawa Wajen Farfado Da Tattalin Arzikin Duniya
Opalola ta bayyana sunan wanda ake zargin jami’in bogi ne na hukumar DSS, Olaleye Oluseyi, mai shekaru 46.
Ta ce wanda ake zargin yana karbar kudi daga hannun mutane ne bisa hujjar sama musu aiki a hukumar DSS.
Kakakin rundunar ta kara da cewa an kama Oluseyi ne a ranar 15 ga watan Janairu, biyo bayan rahoton sirri da aka samu cewa yana bayyana kansa a matsayin jami’in DSS yana yaudarar mutane.
“Ba tare da bata lokaci ba jami’an sa ido na rundunar ‘yansanda suka dauki mataki, suka kama wanda ake zargin, sannan ya amsa laifin damfarar wani Taiwo Victor kan kudi Naira 112,000, bisa nema masa aikin DSS.
“Lokacin da a kama shi, an kuma samu wata hular fuska dauke da rubutun hukumar kiyaye hadura ta tarayya a hannunsa.”
Opalola ta kuma ce an kama wata mata ‘yar shekara 23 da wasu mutane biyu da laifin hada baki da kuma aikata fashi da makami.
Ta ce biyu daga cikin wadanda ake zargin sun zo Osogbo ne daga Legas a ranar 28 ga watan Janairu, inda suka tare a wani otal tare da taimakon matar da ake zargin.
Kakakin ya kara da cewa mutanen ukun sun yi wa wadanda abin ya rutsa da su ne, inda suka yi wa daliban makarantar F
Kwalejin Fasaha ta Ede 20 fashi a gidajen kwanansu.
Ta ce za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.