Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa na 2023.
A safiyar Laraba ne Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu da kuri’u 8,794,726.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Karyata Kalaman Blinken Da Suka Shafi Taiwan
- A Shirye Kasar Sin Take Ta Bayar Da Gudunmuwa Wajen Karfafa Hadin Kan Kasa Da KasaÂ
Tinubu ya doke babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 6,984,520, sai Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 6,101,533 na kuri’u 24,965,218 da aka kada.
Haka kuma, Sen. Rabiu Kwankwaso- na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya zo na hudu da kuri’u 1,496,687.
Da yake mayar da martani kan sakamakon da shugaban INEC ya bayyana, Buhari ya ce: “Ina taya mai girma Bola Ahmed Tinubu murnar nasarar da ya samu.
“Jama’a ne suka zabe shi, shi ne wanda ya fi dacewa da aikin. Yanzu zan yi aiki tare da shi da tawagarsa don tabbatar da mika mulki cikin tsari.”
Shugaba Buhari ya ce duk wanda ke da korafi game da zaben zai iya kalubalantar hukuncin a gaban kotun kararrakin zabe.