Kungiyar masu kiwon kajin gidan gona ta kasa (PFAN) ta ce ‘ya’yanta sun yi asarar sama da Naira biliyan 30 sakamakon karancin sabbin takardun kudi da ake fuskanta.
Shugaban kungiyar na kasa, Sunday Onallo-Akpa ne, ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce matslar na neman durkusar da masana’antarsu.
A cewarsa, masu kiwon sun yi asarar sama da kiret din kwai miliyan 15 saboda lalacewar da suka yi, inda ya sanar da cewa, kwan da aka kyankyashe tun a farkon makon watan Fabirairu 2023, bai wuci kashi 20 a cikin dari aka sayar ba saboda karancin sabbin takardun kudin.
Onallo-Akpa ya kara da cewa, fannin na samar da kashi 25 a cikin dari ga tattalin arzikin Nijeriya, inda kuma fannin ke samar da ayyukan yi ga sama da ‘yan Nijeriya miliyan 25.
Shugaban ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo wa kungiyar dauki don kar ta durkuse.
Ya kuma roki gwamnatin tarayya da ta umarci hukumomi domin su sayi kwan don gudun ka da su kara yin asara.