A uzu billahi minas shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Wa sallallahu alan Nabiyyil karim. Assalamu alaikum warahmtullahi Ta’ala wa barkatuh.
Masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon domin ci gaba da darasinmu kan abin da ya shafi Azumin Ramadan.
- Da Dumi-dumi: APC Ta Dakatar Da Dan Majalisar Wakilai Shehu Koko
- Da Dumi-dumi: APC Ta Dakatar Da Dan Majalisar Wakilai Shehu Koko
Mun shiga goman karshe na watan Azumin bana, wanda ake fatan ‘yan’uwa Musulmi za a kara dagewa domin neman falalar Allah a ciki.
Hadisi ya tabbata daga Uwar Muminai Aisha (RA) cewa “Manzon Allah (SAW) ya kasance idan Goman karshe na watan Ramadan ta shiga, yakan raya dararanta gaba daya (ma’ana ba ya barci), sai ya tayar da iyalansa (su tashi su yi ibada) kuma ya daura mayafinsa (ma’ana kara kokari).
Har ila yau, a cikin dararen ne ake samun babbar garabasar nan ta daren Lailatul Kadri.
Falalar Daren Lailatul Kadri
Lailatul Kadri dare ne mai girma wanda a cikinsa ne Allah (SWT) ya saukar da Alkur’ani. Annabi (SAW) ya yi bayanin cewa ana samun daren a cikin goman karshen Ramadan cikin mara (kwanukan da za a kirga a samu ragowar daya a ciki watau 21, 23, 25, 27, 29).
Abdullah bin Abbas (RA) ya ce “Allah ya saukar da Alkur’ani gaba daya daga Lauhil Mahfuz zuwa sama ta daya a cikin daren Lailatul Kadri.” Daga nan ne Mala’ika Jibrilu ya rika sauko da shi aya-aya ko sura-sura kamar dai yadda Allah ya umurce shi ya yi.
A wani kaulin ana cewa Mala’ika Israfilu ne ya dauko Alkur’anin daga Allah zuwa Lauhil Mahfuz, su kuma Mala’ikun da ake kira da Kiramun Barara suka dauko shi zuwa sama ta daya, daga nan shi kuma Mala’ika Jibrilu ya rika sauko da Wahayinsa ga Annabi (SAW).
Allah Ta’ala ya albarkaci mu al’ummar Annabi Muhammad (SAW) fiye da sauran al’ummomin da suka gabata kamar yadda rayuwar Maigidan namu (SAW) ta fifici ta sauran Annabawa.
A kan haka ne Allah ya ba mu Daren Lailatul Kadri wanda ya fi watanni 1000, kimanin sama da shekara 83. A ko wace shekara, duk Musulmi idan ya yi Ramadan tare da kudurcewa a ransa na samun daren (walau ya gani ko bai gani ba), Allah zai rubuta masa ladan daren. Wannan yana nuna cewa a duk Ramadan, muna da shekara 83 da ‘yan kai kari a kan shekarunmu. Misali, idan mutum ya riski Ramadan sau 40, yana da karin shekaru na ibada dare da rana masu albarka zalla 83 sau 40 wanda zai bashi jimillar shekara dubu uku da dari uku da ashirin (3320). Wannan falala ce ta Allah ga mu al’ummar Annabi (SAW), alhamdulillah.
Wakazalika, saboda falalar da dararan na goman karshe suka kunsa ne ‘yan uwa Musulmi suka zabi yin ibadar Ittikafi a ciki.
Yadda A Ke Ittikafi
Ittikafi (zaman ibada a cikin masallaci dare da rana) Sunnar Manzon Allah (SAW) ce mai girma. Ma’anar ittikafi ita ce koyi da Mala’ikun Allah. Su Mala’iku ba sa ci; ba sa sha, ba sa barci da dare. Haka nan kai ma mai yin ittikafi ba ka ci; ba ka sha da rana, da dare kuma ba ka barci sai ibada. Amma da rana mutum zai iya yin barci.
Ittikafi ba waje ne na surutai da hira da sauran abubuwa na sharholiya ba.
Malamai sun yi bayanin cewa ba a yin ittikafi sai a Masallacin Jumma’a saboda ba a son fita idan an shiga matukar ba a kammala ba; sai idan akwai lalura. Amma wasu Malaman sun ce za a iya yi ko a Masallacin da ba na Jumma’a ba.
Idan mutum ba shi da mai kawo ma sa abinci zai iya fita ya sayo da kansa amma da zaran ya ci kar ya zauna zaman hira. Idan akwai mai kawo ma sa abincin sai kuma ya fita, to ittikafinsa ya baci sai ya sake shiga sabo. Fita daga Masallaci koda da taku kadan ne ba tare da wata lalura ba tana bata ittikafi.
Ana so mai ittikafi ya dukufa da yawan sallolin nafila, da karatun Alkur’ani da Zikiri. Za a iya yin magana a kan ilmi kamar su Tafsiri, Hadisi, Fikhu, Tarihin Annabawa da Waliyyai da sauran Salihan Bayi. Amma ban da irin yadda wasu ke wa’azi na zage-zage a wannan zamanin.
Mai ittikafi zai iya raka wani da ya ziyarce shi amma ba da nisa ba. Mai yi zai rika tsaftace kansa kamar su wanka da wanki, da yanka farce, da aski, da sauran su saboda shi ba kamar wanda ya daura harami ba ne.
Tambihi
‘Yan uwa Musulmi, mu yi kokari mu ci gajiyar dimbin rahamar da Allah (SWT) ya tanadar mana a wannan wata mai albarka. Saboda akwai tsoratarwa daga Annabi (SAW) kan wanda ya kasa aikata wani abu da zai samu rahamar da Allah Ta’ala ya tanada a watan.
Ya zo a cikin wani Hadisin Jibrilu cewa wata rana Annabi (SAW) zai hau mumbari sai aka ji lokacin da ya taka matakala ta farko yana cewa “amin”, da ya taka matakala ta biyu ya sake cewa “amin, aka kara ji a matakala ta uku ya ce “amin.
Da aka tambaye shi a kan amin din da ya yi ta fada sai ya ce “Jibrilu ya fada mun cewa duk wanda ya riski iyayensa biyu amma ya ki yi masu alherin da zai sa su ji dadi su sanya masa albarka ya shiga aljanna; to idan Allah ya sa shi a wuta ya danna shi a can ciki! Na ce amin. Jibrilu ya kara ce mun wanda ya riski Ramadan bai yi abin da Allah zai gafarta masa ba; idan Allah ya sa shi a wuta ya danna shi a can ciki sai na ce amin….”
Don haka idan mutum bai samu damar yin wani abu da zai samu rahama da gafarar Allah ba, to ya yi kokari a wannan goman ta karshe ya yi don ya samu shiga cikin bayin da Allah zai ‘yanta daga wuta da falalarsa musamman ita dama goma ce ta ‘yantarwa daga wuta zuwa aljanna.
A cikin aljannar ma akwai martabobi da mutum zai nema saboda ita hawa-hawa ce. Haka nan Yardar Allah ta fi aljanna baki dayanta dadi, Ganin Allah kuma ya fi su duka kamar yadda ya zo a cikin karatuttuka.
Saboda haka ‘yan uwa mu dage, Allah ya taimaka mana da falalarsa da rahamarsa ya ba mu ikon aikata abin da zai kai mu wurin da aka fi neman mu isa.
Za mu dakata a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi hakka kadirihi wa mikdarihil aziym.