Dangane da taron kolin kungiyar tsaro ta NATO dake tafe, wanda ka iya shafar batun kasar Sin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi karin haske yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa Alhamis din nan, inda ya jaddada cewa, kungiyar tsaro ta NATO ta riga ta lalata kasashen Turai, don haka, ta daina yunkurin kawo cikas ga kasashen yankin Asiya da tekun Pasific da ma duniya baki daya.
Bugu da kari, wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar Amurka ta nuna cewa, kashi 49 cikin 100 na wadanda aka tambaya sun yi imanin cewa, kasar Amurka ba za ta sake zama kasa mai bin tsarin dimokuradiyya ba a nan gaba. Kan wannan batu, Wang Wenbin ya ce, ba wai kawai ana sukar tsarin dimokuradiyya irin na Amurka ba, har ma ta yi kaurin suna a duniya.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, taron zaman lafiya na baya-bayan nan game da yankin kahon Afirka da aka gudanar, wani muhimmin mataki ne ga kasashen Sin da Afirka wajen inganta manufar raya zaman lafiya a kahon Afirka tare. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)