Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Birni a Jihar Kano , Sha’aban Sharada, ya shigar da kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Kano, inda yake neman ta soke takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, a matsayin dan takarar gwamna a 2023 na jam’iyyar APC a jihar.
Dan majalisar wanda ke wakiltar mazabar karamar hukumar Birni, ya bukaci kotun da ta soke zaben saboda zargin aikata rashin adalci yayin gudanar da zaben fidda-gwanin.
- Yadda Noman Rani Ya Rage Kwararowar Mutanen Kauye Zuwa Birni
- Hadin Gwiwar BRICS Ya Kai Matsayin Koli
Duk da zabar Gawuna tare da tsohon kwamishinan kananan hukumomi Murtala Garo da wakilan jam’iyyar APC na Kano suka yi a matsayin ‘yan takarar gwamna, Sharada bai gamsu da zaben ba.
Sha’aban na neman a soke zaben fidda gwanin da aka gudanar na zaben Gawuna a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar, inda ya ce an sabawa dokar zabe ta 2022.
A wata takardar karar da ya shigar gaban babbar kotun tarayya da ke Kano, wanda ya shigar da karar ta hannun lauyansa J. O. Asoluka, SAN, ya ce zabar Gawuna ya sabawa sashe na 84 (1),(3),(8),(12). da (13) na dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.
Bugu da kari, lauyan wanda ya shigar da karar, inda ya bayyana cewa saba tanadin dokar da kuma ka’idojin jam’iyyar APC, gwamnatin jihar ta yi magudin zaben wakilai tare da tilasta musu zaben wanda ba su da ra’ayin zaba.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda zaben fidda gwanin ya gudana wanda ya bai wa masu rike da mukaman siyasa damar kada kuri’unsu duk da sashe na 84 (13) na dokar zabe wanda ya hana su shiga zaben fidda gwani.
A halin da ake ciki, mai shari’a Liman, ya bayar da izinin yin aiki da wasu kararraki biyu da mai shigar da kara ya gabatar.
Kotun ta dage sauraren karar daga kwanaki 30 zuwa kwanaki 15 domin a gaggauta sauraren shari’ar.