Akalla mutane 288 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu sama da 1,000 suka jikkata sakamakon wani hatsari da ya rutsa da jiragen kasa uku a birnin Balasore da ke gabashin jihar Odisha a ranar Juma’a.
Hukumomi a kasar Indiya sun bayyana wannan mummunan lamarin da ya faru da misalin karfe 7 na yammacin ranar Juma’a a matsayin hatsarin jirgin kasa mafi muni a Indiya cikin sama da shekaru ashirin.
- Ko Kun San Laifukan Batsa Da Indiyawa Ke Yi A Bainar Jama’a?
- Kwastam Ta Kama Tramadol Ta Naira Biliyan 1.8 Da Aka Yo Oda Daga Indiya Da Pakistan
Shugaban kasar Indiya, Droupadi Murmu ya wallafa a shafinsa na twitter yana mai cewa “Na yi matukar bakin ciki da samun asarar rayuka a wani mummunan hatsarin jirgin kasa a Balasore. Ina mika gaisuwa ga iyalan wadanda suka rasu. Ina addu’ar samun samun sauki ga wadanda suka jikkata”.
Pradeep Jena, babban sakatare a jihar Odisha ya ce Rukunonin kashe gobara 24 da ‘yan sandan yankin da kuma masu aikin sa kai suna aiki tukuru wajen neman ceto mutanen abun ya ritsa da su.
Indiya, kasa mai mutum biliyan 1.4, tana jigilar akalla fasinjoji miliyan 13 a kowace rana, kimanin mutum biliyan 8 a kowace shekara.