Fiye da wani lokaci, rahoton da aka fitar na matsayin jami’o’in Nijeriya a ma’aunin jami’o’i na duniya ya nuna cewa, wannan ne lokaci fiye da wani lokacin da ake bukatar a maida da hankali a kan halin da harkar ilimi ta ciki a kasar nan musamman ilimin jami’a a kasar nan.
Rahoton da Cibiyar ‘Times Higher Education’ ta fitar ya nuna cewa, gwarzuwar jami’a a Nijeriya ita ce, Jami’ar Afe Babalola (ABUAD) da ke Ado-Ekiti, wadda ta yi ta 400 a jerin jami’o’in duniya.
Cibiyar ta karbu a fadin duniya saboda sahihancin rahotannin da take fitarwa, cikin abubuwan da take lura dasu wajen yanke hukuncin zabar kwazon jami’a sun hada da abin da ya shafi bangaren karantarwa da bincike da kuma yadda jami’ar ta karbuwa a sassan duniya.
Yakamata a fahinci cewa, a shekarar 2022 cibiyar ta nazarci jami’o’i 1, 600 a kasashe 99. Cibiyar ta yi nazarin mukala fiye da Miliyan 108 da kuma kundin bincike da jami’o’i fiye da Miliyan 14.4 ta kuma karbi amsar tambayoyi daga masana fiye da 22,000 a fadin duniya.
Babu wata kasar Afrika data zo cikin jami’o’i na 100 na farko a jerin gwarazan jami’o’i duniya. Gwarzuwar jami’a data fi tsari a Afrika ita ce jami’ar kasar Afirka ta Kudu ‘Unibersity of Cape Town’ inda ta zo ta 183 a duniya. A Nijeriya kuma Jami’ar Ibadan da ta Legas suka zo na 401 da 501.
A yayin da muke taya Jami’ar ABUAD murnar wannan nasarar, mun lura da cewa, wannan yana nuna irin tsananin yadda harkar ilimi ta tabarbarewar a kasar nan.
Duk da matukar muhimmancinta a wajen tafiyar da tattalin arzikin kasa gwamnatocin da suka gabata sun yi watsi da harkar ilimi, ta hanyar nakasa kasafin kudin da ake tanadar wa bangaren ilimin.
Akwai bukatar a sake nazarin kasafin kudin da jihohin kasar nan 36 ke samar wa bangaren ilimi musamman ma ganin kowacce jiha a halin yanzu ta mallaki jami’a ta kanta. Yayin da hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a ware kashi 25 na kasafin kudin da aka kiyasta kashe ga bangaren ilimi har yanzu Nijeriya bata kai ga samar da kashi 15 ba.
A kasafin kudin shakarar 2022 gwmanatin Nijeriya ta ware wa bangaren ilimi Naira Tiriliyan 1.29 wanda ke nuna cewa kashi 7.9 kenan na kasasfin kudin da aka yi a shekarar. Wannan na nuna cewa an yi wa bangaren ilimi kashi 10 kenan duk kuwa da cewa, Majalisar Dinkin Duniya ta nemi ne aware kashi 25 na kasafin kudin a duk shekara don tallafa wa harkar ilimin al’umma.
Idan za a iya tunawa gwamnatin Buhari ta kasafta kashe Naira Tiriliyan 55.3 don gudanar da harkokin gwamnati a cikin shakara 6 na mulkinta amma Naira Tiriliyan 3.5 kawai aka ware wa bangaren ilimi wanda ke nuna kashin yana kasa da kashi 10, wanda ke nuna karara lamarin ilimi ba abin da gwamnatin ta dauka da muhimmanci bane.
Abin takaici a nan shi ne bangaren ilimi ya yi fama da matsalar kudade ga rashin kayan aiki da kuma karancin albashi ga kuma karancin ma’aikata wanda duk suna taimakawa wajen haifar da matsaloli ga bangaren ilimin tun daga firamare, sakandare har zuwa manyan makarantu.
Yawancin masana a bangaren ilimi basu yi mamakin ganin jami’o’in Nijeriya basu tabuka abin a zo a gani ba a tantancewa tare da matsayin su a tsakanin jami’o’in duniya, wannan yana faruwa ne saboda yawan yajin aikin da malaman jami’a ke shiga wanda ke haifar da cikas a abin da ya shafi bincike da karantarwa, fiye da wata 4 kenan malaman jami’o’i a Nijeriya ke yajin aiki har yanzu ba a kai ga warware matsalar ba.
A karkashin wannan gwamnatin kawai Malaman Jami’a sun yi yajin aiki na fiye da wata 13, wannan ba karamin asara ba ne ga harkar ilimi a Nijeriya.
Wadannan na daga cikin matsalolin da suka haifar da tabarbarewar ilimi a kasar nan kuma in har ba a magance su ba lamarin ilimi zai cigaba da tabarbarewa a kullum, hakan kuma abin kunya ne ga Nijeriya a idon duniya.