Gwamna Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi ƙwaƙƙwaran bincike kan sulhu da ake yi da ‘yan bindiga a Jihar Zamfara.
Rahotonni sun bayyana yadda wata tawaga ta gwamnatin tarayya take gudanar da zaman sulhu da ‘yan bindiga a Zamfara, ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.
- Babu Sulhu Tsakaninmu Da ‘Yan Fashin Daji -Gwamnatin Zamfara
- Sace Daliban Zamfara: Matawalle Ya Bayar Da Tabbacin Dawowarsu Cikin Koshin Lafiya
Mataimaki na musamman kan yada labarai na gwamna Dauda, Suleman Bala Idiris, ne ya bayyana haka a takardar da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin.
A cewarsa gwamnatin Zamfara ta yi Allah wadai da tawagar da gwamnatin tarayya ke jagorantar wannan sulhu, ba tare da tuntuɓar gwamnatin jihar ba.
Kakakin gwamnan, ya ƙara da cewa, Gwamna Lawal, ya nemi Glgwamnatin tarayya da ta yi bincike tare da yin bayani kan wannan sulhu, domin yin hakan ya saɓa da matsayar da gwamnatinsa ta ɗauka tun da farko.
Ya ce: “Gwamna Dauda Lawal yana neman ƙarin bayani daga gwamnatin tarayya kan sulhun da wasu waɗanda suka kira kansu wakilanta suke aiwatarwa a Jihar Zamfara.
“Gwamnatin Jihar Zamfara ta samu rahotanni cewa waɗannan wakilai na gwamnatin tarayya sun yi zaman sulhu da ‘yan bindiga a Birnin Magaji, Maradun, Mun Haye, Ajah, Bawo, da kuma Bagege.
“Sanin kowa ne, gwamnatocin baya da suka gabata a Jihar Zamfara sun jaraba yin sulhu da ‘yan bindiga, kuma abin bai haifar da ɗa mai ido ba.
“A dalilin haka ne gwamnatin Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta bayyana matsayarta tun farko cewa, babu ranar yin sulhu da ‘yan bindiga.
“Wannan matsaya ce da aka ɗauka domin tabbatar da an yaƙi wannan ɓarna gabaɗayanta. Kuma muna ganin nasarorin da ake samu ba ta hanyar yin sulhu ɗin ba. Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta dakatar da wannan sulhu, domin ba alheri ba ne ga al’umman Jihar Zamfara.” Cewar sanar gwamnatin jihar ta bakin Sulaiman.