Daya daga cikin hazikan marubutan littattafan Hausa na yanar gizo wato FATIMA SUNUSI RABI’U wacce aka fi sani da UMMU AFFAN, ta bayyana wa masu karatu dalilinta na fara rubutun littafin Hausa tare da irin nasarorin da ta samu game da rubutun, har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU kamar haka:
Ya sunan malamar?
To cikakken sunana shi ne; Fatima Sunusi Rabi’u, amma a ‘media’ an fi sani na da Ummu Affan.
Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
An haife ni a shekarar Alif da dari tara da casa’in da bakwai (1997), a Jihar Katsina karamar hukumar Funtuwa. Na yi karatuna tun daga firamare zuwa karamar Sakandare a can, yayin da rayuwata ta dawo garin Kaduna anan na dora daga SS 1 har nayi kandi a 2015. Karatun addini ma Alhamdulillah nayi sauka sannan kuma ina da aure ma.
Me ya ja hankalinki har kika fara rubutu?
To gaskiya da farko sha’awa ce, domin tun ina karama nake sha’awar rubutu. Sannan na kasance makaranciyar littattafan Hausa hakan ne ma ya kara sa mini jin sha’awar rubutun har nake jin zan iya. Na kan sami littafi guda da biro na rubuta labari. A da, ina rubutawa na tara da niyyar watarana zan buga, kafin daga baya na ga ana rubutu a online ni ma na ce bari to na fara a nan.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
To Alhamdu lillahi ban sha wata wahala ba, kasancewar a midiya nake rubutun nawa, duk da dai da farko ni kadai nake fostin har daga baya kuma na ga wasu ma suna taya ni ba tare da na sani ba, to sai dai hamdala.
Ya batun iyaye lokacin da kika fara sanar musu kina son fara rubutu, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Ban fuskanci kalubale ba, don tun ina gida mahaifiyata na kara mini kwarin gwiwa. Shi ma mahaifina ban samu matsala da shi ba, ban sani ba ko dan sai da na yi aure sannan na fada masa ina rubutun tunda da ina gida ban buga ba sai bayan aurena na fara rubutu a Online.
Ya farkon fara rubutun ya kasance?
Gaskiya da farko ban sha wahala sosai ba, tun da ni ‘Online Writer’ ce, nakan yi rubutu ne kuma na tura, tun littafina na farko gaskiya Alhamdu lillah ya samu karbuwa sosai.
Kamar wanne bangare kika fi maida hankali akai wajen yin rubutu?
Ina rubutuna a kan rayuwar yau da kullum, fadakarwa, soyayya, nishadi da sauransu, maganar gaskiya babu inda bana tabawa indai na sami jigo to zan rubutu a kai domin masu irin abin su wa’azantu.
Kin rubuta labarai sun kai kamar guda nawa?
Eh! to gaskiya na rubuta labarai a kallah guda goma sha takwas 18, bayan gajerun labarai na shiga gasa da na dan rubuta a kalla bakwai.
Wanne labari ne ya zamo bakandamiyarki cikin wadanda ki ka rubuta?
Duka littattafaina ina kaunarsu kam, amma zan iya cewa ‘MU GANI A KASA…’ Yanzu shi ne bakandamiyata.
Wanne labari ne ya fi baki wahala wajen rubuta shi?
Littafina ‘SANDAR MAKAUNIYA’ kasancewar akwai siyasa a cikin labarin da tsaface-tsaface da kuma aljanu na dan sha wahala, musamman a kan aljanin da ke jikin yarinyar tun da ba jinsina ba ne, na dan sha wahala wajen ganin na rubuta abin da yake tamkar a zahiri.
Cikin labaran da ki ka rubuta ko akwai wanda ki ka buga?
Eh Alhamdu lillah akwai wata gasa da aka saka wani malaminmu ne a nan online na shiga cikin mutum biyar da aka buga wa labaransu, an buga mini BAKAR FURA… kuma ni ma na saka kudi aka kara yi min wasu, daga baya kuma na buga MU GANI A KASA… shi ma.
Za mu ci gaba mako mai zuwa