Maimartaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya isa Kano domin karbar takardar nadinsa a karo na biyu daga Gwamna Abba Kabir Yusuf. Bikin wanda aka shirya gudanarwa da misalin karfe 10 na safe a gidan gwamnati, zai hada da jawabai daga gwamna da mai martaba sarki, sai kuma sanarwar mubaya’a daga Hakimai da masu rike da sarautar gargajiya.Â
A safiyar ranar Alhamis ne aka samu rahoton dawo da Sanusi II, kuma an sa ran zuwansa Kano a safiyar Juma’a. Taron gabatarwar zai kunshi manyan jami’an gwamnatin jihar da sarakunan gargajiya.
- Gwamantin Kano Ta Hana Tsohon Sarki Aminu Ado Dawo Wa Jihar KanoÂ
- Da ÆŠumi-É—umi: Gwamna Yusuf Ya Mayar Da Sanusi II A Matsayin Sarkin KanoÂ
A kwanakin baya ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da gyaran kudurin dokar majalisar masarautun Kano ta shekarar 2024 da aka yi wa kwaskwarima, wadda gwamnan ya sanya wa hannu. Hakan ya mayar da masarautar Kano matsayinta na da tun kafin shekarar 2019 tare da rusa sabbin masarautun Gaya da Rano da Karaye da Bichi guda hudu, wanda ya kai ga dawo da Sarki Sanusi II.
Taron dai ya gudana ne duk da umarnin wucin gadi da wata babbar kotun tarayya ta bayar na umarnin a tabbatar da zaman lafiya a jira ta yanke hukunci ranar 3 ga watan Yuni mai kamawa, wanda ya nuna irin sarkakiyar da ke tattare da batun dawo da Sanusi II.