Wani kamfani mai suna ‘Haril Global Solutions Limited’ ya bukaci Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ya umarci Bankin Globus ya biya shi Naira biliyan 10 a kan karya yarjejniyar bashi da suka yi tsakaninsu.
A takardar sammacin karar mai lamba CB/1456/2024, kamfanin ya yi bayanin cewa, bankin ya cire masa wasu kudade daga asusun ajiyarsa ba tare da izinin su ba, wanda hakan ya karya ka’ida da sharuddodin da aka cimma wajen bayar da bashin tun da farko.
- Hukumar Yaki Da Shan Maganin Kara Kuzari Yayin Wasanni Ta Duniya Ta Fallasa Ayyukan Amurka Game Da ’Yan Wasa Masu Keta Ka’idoji
- Gwamnatin Tinubu Na Ƙoƙarin Gyara Kurakuran Baya, Ba Jawo Wahala Ba – Minista
Lauyan kamfanin, Pelumi Olajengbesi Esk., ya bayyana cewa, duk da karya yarjejeniyar kwangilar, sai kuma gashi bankin ya rubuta wa wasu bankuna wasika yana bata sunan kamfaninmu, bankunan da ya rubutawa takardar bantanci sun hada da Access Bank, Fidelity Bank, da kuma Wema Bank.
A kan haka ne wadannan bankunan suka bayar da umanin dakatar da amfani da asusun ajiyar kamfanin a bankunan su.
A takardar rantsuwa da wani babban daraktan kamfanin mai suna Oluwaseun Onobun ya sanya wa hannu, ya yi bayanin cewa, a ranar 7 ga watan Disamba na shekarar 2021, bankin Globus ya aiko musu da wasikar amincewa da basu bashin N500,000,000.00 don kamfaninmu ya tayar da komatsar jarin mu da ya yi kasa, an kuma shirya biyan kudaden a cikin shekara daya.
Ya ce, wasikar ya samu sa hannun dukkan jami’an bankin, wanda ke nuna amincewa daga Bankin Globus.
Daga nan ya kuma bayyana cewa, cikin ka’idar bashin akwai cewa, za a cire ruwan kashi 16 a cikin dari, za kuma a fra cire kudin bashin ne bayan akalla wata 2 da karbar bashin.
A kan wannan karya yarjejeniyar ne kamfanin ya nemi kotu ta bai wa bankin umarnin biyan diyyar Naira miliyan10 tare da kuma tilasatawa bakin biyan miliyoyin naira da suka cire daga asusun ajiyar kamfanin ba tare da ka’ida ba.
A martaninsu, Bankin ya karyata dukkan ikirarin da kamfanin ya yi, a jawabinsa, lauyan bankin, Tamunosiki Wakama ya nemi kotun ta yi watsi da dukkan bukatun da bankin ta gabatar domin basu da muhimmanci.
Daga karshe kotun ta daga sauraron karar zuwa ranakun 13 da 14 na watan Janairun shekarar 2025.